Gwamnoni Sun Fara Kumfar Baki a Kan Tallafin da Shugaba Tinubu Ya Rabawa Jihohi

Gwamnoni Sun Fara Kumfar Baki a Kan Tallafin da Shugaba Tinubu Ya Rabawa Jihohi

  • Gwamnatin tarayya ta rabawa duka jihohi tallafin biliyoyin kudi saboda an shiga matsin lamba
  • Daga baya sai gwamnonin su ka fahimci cewa za su rika biyan bashin duk abin da aka raba masu
  • Wannan ya jawo rashin jituwa tsakanin gwamnatocin jihohi da tarayya a karkashin Bola Tinubu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wasu daga cikin gwamnonin kasar nan da ke karkashin NGF sun ki amincewa da umarnin da gwamnatin tarayya ta ba kungiyarsu.

This Day ta ce tallafin da Bola Ahmed Tinubu ya amince a rabawa gwamnatocin jihohi ya jawo sabani bayan surutun da sauran jama’a su ke ta yi.

A makon jiya aka samu labari gwamnatin tarayya ta rabawa duka jihohi 36 tallafin N5bn domin a rage radadin yadda jama’a su ke ciki a halin yanzu.

Gwamnoni da Shugaba Tinubu
Bola Tinubu da Gwamnonin Jihohi Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya na kokarin kawo sauki

Kara karanta wannan

Murna ta Koma Ciki, Kudin Tallafin da Tinubu Zai ba Jihohi bashi ne ba Kyauta ba

Sakamakon tsadar fetur da aka janyewa tallafi tun Mayu da kuma tashin farashin kayan abinci, gwamnatin kasar na neman kawowa talaka sa’ida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanaki da yin maganar rabon kudin, jaridar ta ce an samu gwamnonin da ke ganin babu dalilin da za a bukaci su biya abin da tallafi ne ga talakawa.

Tallafin Tinubu bashi ne ba kyauta ba

Ita dai gwamnatin Bola Tinubu ta ce duk gwamnan da ya karbi tallafin, zai biya bashi daga baya, hakan bai yi wa wasu ‘yan kungiyar ra NGF dadi ba.

Akwai gwamnonin da su ka yi fushi da shugabansu, Mai girma AbdulRahman AbdulRazaq saboda amincewa da sharudan da aka gindayawa NGF.

A karshen taron ranar Laraba, sai dai gwamnonin su ka watse ana ta ihu ba tare da cin ma matsaya ba duk da an fara taron tun 10:00 zuwa 3:00 na dare.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC Ta Ki Amincewa Da Shirin Ba Wa Gwamnoni N5bn Na Tallafi, Ta Fadi Dalilai

Labarin da aka samu daga The Cable shi ne an ajiye siyasa a gefe da ake tattaunawa kan rabon. Akwai gwammnoni a APC, PDP, LP, APGA har da NNPP.

'Yan NGF za su ja daga da gwamnati

Majiyoyi dabam-dabam sun tabbatar da cewa abin da ya jawo sabanin shi ne wata sanarwa da ta fito daga Darekta Janar na NGF, Asishana Okauru.

Wani gwamna ya shaida cewa ba su amince a rika cire masu N120,000,000.00 a duk wata domin su biya wannan kudi ba alhali tallafi ne ga talakawa.

Nadin sababbin Ministoci

Ku na da labari Bola Tinubu ya dauki aro a wajen tsohon shugaban Najeriya, bai bada babbar kujerar Ministan fetur ba, shi ne zai rike wannan kujera.

Kusan duk Ministocin Abuja da aka yi daga Arewa su ka fito tun daga 1979, a karon farko mutumin Kudu watau Nyesom Wike. zai hau kujerar a bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel