Shugaba a APC Ya Tona Yanayin da Tinubu Ya Iske Tattalin Arziki a Hannun Buhari

Shugaba a APC Ya Tona Yanayin da Tinubu Ya Iske Tattalin Arziki a Hannun Buhari

  • Adams Oshiomhole ya yi Allah-wadai da yadda Bola Ahmed Tinubu ya samu halin tattalin arziki
  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce yanayin kasar ta jawo ake daukar tsauraran matakai
  • Bola Tinubu ya gaji tulin bashi daga hannun Muhammadu Buhari wanda ya shekara takwas a ofis

Abuja - Adams Oshiomhole mai wakiltar Edo ta Arewa a majalisar dattawa, ya koka kan yadda Bola Ahmed Tinubu ya tsinci mulkin kasar nan.

Da yake jawabi a fadar shugaban kasa, Vanguard ta rahoto Adams Oshiomhole ya na mai cewa ba za a iya shawo kan tattalin arziki da gaggawa ba.

Ganin yadda ake fama da tattalin arzikin Najeriya bayan Bola Ahmed Tinubu ya shiga ofis, Sanata Arewacin Edo ya kare sabon shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

Buhari ya damkawa Tinubu mulki
Shugaba Muhammadu Buhari da Bola Tinubu Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Adams Oshiomhole ya hadu da Kashim Shettima

Bayan haduwarsa da Kashim Shettima a Aso Rock, Sanata Adams Oshiomhole ya ce ya zama dole a dauki matakai masu tsauri domin a gyara tattali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Batun tattalin arzikin kasa aiki ne da aka soma. Babu dabarar shawo kan lamarin da wuri. Gwamnati ta gaji mummunan yanayin tattali.
Kowa ya sani. Gwamnati ta karbi tattalin arzikin da duka kudin shigarmu kusan bai isa wajen biyan bashin da ya ke kan wuyan Najeriya.
Babu abin da ya fi muni irin haka. Amma sun zo da jajircewa cewa za su canza yadda abubuwa su ke tafiya; su shawo kan tattalin arzikin.
Wasu matakai masu zafi sun zama dole ne. Tamkar yadda duk wani daga cikinmu ya taba rashin sa’a za ayi masa aikin fida ne a jikinsa.
Idan ana so ayi lambo, za a iya amfani da mai, turare, a daura babban riga, a rufe cutar. Amma likitan kwarai zai ce ana bukatar fida."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zauna da Gwamnan CBN Sakamakon Tsinkewar Farashin Dala a Kasuwa

- Adams Oshiomhole

Buhari ya jawo bashi ya kwashe komai

The Cable ta rahoto tsohon shugaban na APC ya na bayanin yadda 96% na abin da ya shigoowa Najeriya ya bi iska domin biyan bashin da aka karba.

Idan N100, 000 su ka shiga asusun Najeriya, za ayi amfani da N96,000 a biya bashin da aka ci, hakan ya nuna ya zama dole a nemo hanyar samun kudi.

Za a cefanar da NNPC a Najeriya

A haka ne aka samu labari Gwamnatin Bola Tinubu za ta cefanar kayan gwamnati nan da shekara daya da rabi saboda a samu kudin more rayuwa.

MOFI ta ce wasu daga cikin kamfanonin su na bukatar ‘yan kasuwa su samu mafi yawan hannun jari, a maimakon mallakar kason da bai da amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel