Bashin da Ake Bin Najeriya Yakai Naira Tiriliyan 46 da Biliyan 25

Bashin da Ake Bin Najeriya Yakai Naira Tiriliyan 46 da Biliyan 25

  • Najeriya ita ce kasa mafi arzikin man fetur a Nahiyar Afrika, wanda hakan ke nufin kudi masu shigowa da yawa
  • Duk da wannan baiwar da Allah ya bawa Najeriya tana fama da cin bashi domin ayyukan raya ƙasa
  • Yanzu haka, bashin ƙasar yakai adadin Tiriliyan 46 da Biliyan 25 inji DMO

Abuja - Bashin da ake bin Najeriya yanzu haka yakai adadin Tiriliyan 46.25 a ƙarshen Disemba na shekarar 2022.

Hakan na zuwa ne ta bakin Ofishin dake Kula Bashi na Ƙasa (DMO).

DMO ya saki wasu alƙaluma a wannan rana dake nuni da yadda ake bin gwamnatin tarayya, dana Jihohi da babban birnin tarayya bashi.

DMO Abuja
Emma Ujah, Abuja Bureau Chief Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Najeriya ita ce kasa mafi arzikin man fetur Afrika

Kara karanta wannan

Akwai Yunwa: Gwamnatin Tarayya Da Bayyana Adadin Yaran Dake Galabaita a Najeriya Saboda Rashin Abinci Mai Kyau

Duk da wannan baiwar da Allah ya bawa Najeriya tana fama da cin bashi domin ayyukan raya ƙasa

Yanzu haka, bashin ƙasar yakai adadin Tiriliyan 46.25 inji DMO

Bashin da ake bin Najeriya yanzu haka yakai adadin Tiriliyan 46.25 a ƙarshen Disemba na shekarar 2022 kamar yadda wani wani rahoton Vanguard ya nuna.

Hakan na zuwa ne ta bakin Ofishin dake Kula Bashi na Ƙasa (DMO).

DMO ya saki wasu alƙaluma a wannan rana dake nuni da yadda ake bin gwamnatin tarayya, dana Jihohi da babban birnin tarayya bashi.

Alƙaluman sun nuna cewa, adadin bashin da ake bin Najeriya a watan Disamba 2022 yayi sama da Tiriliyan N6.69 idan aka haɗa da yadda bashin yake a Disemba na 2021, wanda ya tsaya a Tiriliyan N39. 56 a wancan lokaci kamar yadda Jaridar Punch itama ta ruwaito.

Ofishin kula da cin bashin yace, bita da akayi na bashin ya nuna an samu cigaba na adadin da kaso 23.20% na babban Samfurin cikin gida dake nuna tattalin arziki (GDP). Rahoton Premium times.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

Hakan na nuna tsarin tattalin arziki na kan hanya kamar yadda gwamnatin tarayya ta tsara da kuma ƙungiyoyi, da hukumomin ƙasa da ƙasa.

"Kaso 23.20% da aka samu na GDP, na tafiya daida a cikin tsarin 40% da Nigeriya ta gindayawa kanta, wanda yake daidai da 55% na Hukumar bada lamuni ta duniya IMF, da kuma kaso 70% da ƙungiyar ƙasashen Afrika ta yamma ta sakawa mambobin su".

Jerin Kasashe Biyar da Suke Bin Najeriya Bashi na Kuɗaɗe Maɗuɗai

Wani labari mai kama da wannan, Najeriya ta zama ƙasa da take cin bashi daga kasashen duniya daban daban domin yin ayyukan raya ƙasa.

Kamar yadda ake zato, China ita ce a gaba gaba duk a cikin rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel