Ba Halin Musulmi Bane: CAN Ta Soki El-Rufai Kan Kalamansa, Ta Ce Maganarsa Ba Ta da Alaka da Musulmai

Ba Halin Musulmi Bane: CAN Ta Soki El-Rufai Kan Kalamansa, Ta Ce Maganarsa Ba Ta da Alaka da Musulmai

  • Kungiyar Kiristoci (CAN) a jihar Kaduna ta caccaki tsohon Gwamna Nasir El-Rufai kan kalamansa a wani faifan bidiyo
  • Shugaban kungiyar reshen jihar, Joseph Hayab ne ya yi wannan suka yayin hira da gidan talabijin na Arise
  • Hayab ya ce El-Rufai yana magana ne a radin kansa ba wai don mutanen jihar Kaduna ko musulmansu ba

Jihar Kaduna – Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna ta soki tsohon Gwamna Nasir El-Rufai kan kalamansa da ya yi a kan tikitin Muslim-Muslim.

Shugaban kungiyar reshen jihar, John Joseph Hayab ne ya fadi haka a ranar Laraba 7 ga watan Yuni.

CAN ta caccaki El-Rufai kan kalamansa na Muslim-Muslim
Tsohon Gwamna El-Rufai Na Kaduna. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Joseph Hayab a wata hirarsa da gidan talabijin na Arise, yace El-Rufai ya na magana ne akan radin kansa amma ba da yawun ‘yan jihar Kaduna ko Musulmai ba.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba Ahmed Ya Caccaki Tikitin Muslim-Muslim, Ya Ce Yaudara Ce, Kuma Bai Amfani Musulman Ba

El-Rufai ya ce tikitin Muslim-Muslim ya taimaka musu wurin sake kafa gwamnati

A wani faifan bidiyo da ya yadu a makon da ta gabata, an gano Nasir El-Rufai yana cewa tikitin Muslim-Muslim shi ya taimaka suka sake kafa gwamnati a jihar da kuma nasarar Bola Tinubu, cewar Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan yana magana ne a yayin ganawa da wasu malaman Muslunci da yaren Hausa inda yake cewa:

“Duk da taron dangin kabilanci da na addini da aka mana, Allah ya bai wa Bola Tinubu nasara a zaben.
“Kuma a jihar Kaduna ma mun yi nasara da tikitin Muslim-Muslim wanda ya zama har a kasa baki daya.”

Hayab ya maida martani mai zafi

Punch ta tattaro martanin Hayab yana cewa:

“Faifan bidiyon na gaskiya ne, haka El-Rufai yake, idan ka sanshi shekaru 20 kuma ka kalli bidiyon kasan shi ne, El-Rufai ba zai sauya ba.

Kara karanta wannan

An Gagara Shawo Kan Tsohon Gwamnan APC, Ya Dage da Neman Shugabancin Majalisa

“Bari in fayyace komai, tunanin cewa Tinubu ya yi nasara saboda wannan, ya nuna cewa har yanzu yana rayuwa ta jin shi mai kaskanci ne, yana ji cewa mutane sun raina shi, suna ganin ba zai iya yin wani abu ba, wannan shi yake sa shi yake yin wasu abubuwa don ya nuna yana da iko."

Ya kara da cewa:

“Kowa ya sani nasarar Tinubu duk da wasu suna kotu har yanzu, bai shafe mu ba, wannan nasara har da Kiristoci a ciki wurin ba da gudumawarsu
“Jihar Benue kashi 90% Kiristoci ne, amma Tinubu ya ci zabe a can, ta yaya mutum zai ce wai Kiristoci basu zabe shi ba, haka jihar Rivers, za ka ce babu kuri’un Kiristoci a can, ka je ka duba duk sauran jihohin ka gani.

El-Rufai Ya Zargi Tsoffin Gwamnonin Jihar da Satar Kudaden Al’umma Don Gina Gidaje a Dubai

A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi tsoffin gwamnonin jihar da satar kudade.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Dauki Zafi Bayan Gano Yaudarar da Aka Yi Wajen Shigo da Jirgin Nigeria Air

Gwamnan ya bayyana haka ne a ganawarsa ta karshe a matsayin gwamna, inda ya ce barayin sun gina gidaje a Dubai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel