Dalilin da yasa ba zan saki El-Zakzaky ba – El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce ba zai saki Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria, (IMN), wacce aka fi sani da shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ba saboda radadin da shi da magoya bayansa suka sanya a zukatan mutanen jihar Kaduna tsawon shekaru 30 kafin a kama shi.
El-Rufai wanda ya yi magana a wata hira da gidan radiyo a ranar Juma’a, ya yi bayanin cewa makomar Shugaban kungiyar ta IMN baya a hannun gwamnatin jihar Kaduna cewa a hannun kotu ya ke.
Ya ce abunda gwamnatin tarayya ke nufi lokacin da ta ce makomar El-Zakzaky na a hannun gwamnatin jihar Kaduna shine cewa ba ita bace a kotu da Shugaban na IMN a yanzu.
Gwamnan ya yi bayanin cewa bayan gwamnatin tarayya ta kama tare da tsare Shugaban na IMN a 2015, gwamnatin jihar Kauna da ta tuna zargin laifuffukan da Shugaban na IMN da magoya bayansa suka aikata a kan mutane da gwamnati tsawon shekaru 30, sai ta gudanar da wani bincike cikin rashin bin dokarsu, cin zarafin sauran mutane daga lokacin da suke birnin Zaria har zuwa lokacin da suka dawo Gellesu Quarters.
A koda yaushe mambobin IMN basa yarda da aikata laifi maimakon haka sai suka zargi gwamnati da kai masu hare-hare.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa Alkalin tarayya, Justis Ibrahim Maikaita Bako rasuwa
Gwamnan ya ce duk kungiyoyin kasashen waje da suke sanya baki a lamarin suna bata wa kansu lokaci ne domin cewa wahalhalun da El-Zakzaky da mutanensa suka sanya mutanen Kaduna ciki yana da yawa on haka gwamnatin jihar ba za ta sake shi ba har sai kotu ta yanke hukunci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng