Kotun Zabe: Muhimman Abubuwa 5 Da Ka Iya Sa a Tsige Tinubu Daga Shugabancin Najeriya

Kotun Zabe: Muhimman Abubuwa 5 Da Ka Iya Sa a Tsige Tinubu Daga Shugabancin Najeriya

  • Shugaban Tinubu zai san makomarsa nan ba da jimawa ba yayin da kotun sauraren kararrakin zabe ta tunkari matakin karshe
  • An shigar da korafe-korafe da dama a gaban kotun inda manyan alkalai guda biyar ke jagorantar shari'ar
  • Paul Ibe, mai bai wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP shawara ta fuskar yada labarai, ya shaidawa Legit.ng cewa, shaidun da ke gaban kotu sun isa a yi hukunci na adalci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja A yayin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta kusa kai ga matakin karshe, idanuwa na kan kwamitin mutane biyar na kotun daukaka kara.

Ana jira su yanke hukunci na karshe bayan gabatar da shaidu da dama, gami da hujjoji masu kwari da masu shigar da kara suka gabatar.

Sai dai ‘yan Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana, cike da fargaba wajen jiran hukuncin shari’ar da ta fi kowace muhimmanci a tarihin dimokuradiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: FG Da NLC Sun Fara Tattaunawa Kan Shirin Rage Radadi Na Tinubu Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

Abubuwa biyar da ka iya sanyawa a tsige Tinubu
Wasu muhimman abubuwa guda biyar da ake ganin za su iya sa a tsige Tinubu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu na ganin cewa kotu za ta iya sauke shugaba Tinubu daga kan karagar mulki duba da irin hujjojin da aka gabatar yayin shari'ar.

A cikin wannan makala, Legit.ng ta tattaro wasu manyan abubuwa biyar da ake ganin za su iya janyowa shugaban rasa kujerarsa.

1. Zargin rashin gudanar da ingantaccen zabe

Wannan dai batu ne da aka shafe watanni ana yi tun bayan kammala zaben shugaban kasa.

Wasu masana harkokin siyasa da masu sharhi kan al'amuran jama'a, sun zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), da rashin gudanar da ingantaccen zaben shugaban kasa.

A baya-bayan nan ne kuma ka jiyo tawagar masu sa ido kan zabuka ta Tarayyar Turai (EU), ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa zaben ya rasa inganci da sahihanci.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Atiku Zai Halarci Zaman Kotun Kararrakin Zabe Don Gabatar Da Kara Ta Karshe, Bayanai Sun Fito

Rahoton ya kuma bayyana cewa akwai shakku akan wasu daga cikin jami’an hukumar ta INEC, ciki kuwa har da shugabanta.

Mai taimakawa Atiku kan harkokin yaɗa labarai Paul Ibe, ya shaidawa Legit.ng cewa sun gabatar da shaidu a gaban kotu da ke tabbatar da cewa zaɓen da aka yi cike yake da maguɗi.

2. Zargin fataucin miyagun kwayoyi

Wannan batu ne da ya dade ana ta kai kawo a kansa, wanda yana cikin abubuwan da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zaben.

An tattaro cewa tawagar lauyoyin Tinubu ta amince a kotun cewa, ya taba yin bayar dala 460,000 ga gwamnatin Amurka bisa laifin safarar miyagun kwayoyi da kuma karkatar da kudade.

A jawabin karshe na Atiku, ya bayyana karara cewa saboda wannan amsa laifin da Tinubu ya yi, babu dalilin tsayawa takarar shugabancin Najeriya, balle a ayyana shi a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hanyoyi 4 na kare kai daga fadawa ta'addanci bayan cire tallafin man fetur

3. Shaidar zama dan kasa biyu

A wani bangare na karar da Atiku ya shigar da kuma shaidun da aka gabatar a gaban kotun, an zargi shugaba Tinubu da mallakar fasfo din dan kasar Guinea.

Wani rahoto da Legit.ng ta wallafa a baya, ya nuna cewa kungiyar lauyoyin Shugaba Tinubu ta amince cewa yana da fasfo din wata kasa.

Sai dai kuma hujjar da suka gabatar a kotu, ta bayyana cewa tun shekarar 2020 Shugaba Tinubu ya soke katin dan kasar.

Koke-koken da aka shigar a gaban kotun sun bayyana cewa hakan cin zarafi dokokin zabe ne da ya kamata a yi la’akari da shi wajen hana Tinubu takara.

4. Juyin mulkin Nijar da gwagwarmayar ECOWAS

Tinubu, wanda a halin yanzu yake shugabantar ECOWAS, ga dukkan alamu yana fuskantar kalubale wajen ba da umarni a yankin.

Tinubu ya bayar da umarnin mayar da mulki hannun farar hula cikin kwanaki bakwai, amma sai gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta yi kunnen uwar shegu da shi.

Kara karanta wannan

Jar miyan matasa: Tinubu zai sama wa 'yan Najeriya aiki a Google, ya fadi ta yaya

Su ma shugabannin sojoji na Mali da na Burkina Faso, sun gargadi Shugaba Tinubu kan tsoma baki cikin harkokin Nijar.

5. Atiku ya lashe jihohi 21 a lokacin zabe

Wannan wani muhimmin lamari ne da Atiku da PDP ke ci gaba da matsawa kotun wajen yin amfani da shi a yanke hukunci.

Kamar yadda yake kunshe a cikin jawabin karshe na Atiku, ta bakin babban lauyansa, Chris Uche SAN, ya bayyana cewa har yanzu batun bai samu wani cikas ba a cikin shari'ar da ake gudanarwa.

Ana hasashen cewa wannan batu na lashe jihohi 21, zai zama muhimmi abu a hukuncin karshe da kotun za ta yanke.

MURIC ta bukaci Tinubu ya bai wa Musulmin Najeriya bashi mara ruwa

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan bukatar da kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta mika ga Shugaba Bola Tinubu dangane da bayar da bashi.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: Yan Sanda Sun Yi Ram Da Matasa 6 Kan Fashi Da Makami a Bauchi

MURIC ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta samar da tsarin bayar da bashi mara ruwa ga Musulmin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel