Tinubu Zai Hada Kai da Kamfanin Google Domin Kirkirar Ayyuka Ga ’Yan Najeriya, Musamman Matasa

Tinubu Zai Hada Kai da Kamfanin Google Domin Kirkirar Ayyuka Ga ’Yan Najeriya, Musamman Matasa

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na son hada hannu da kamfanin Google wajen samar da ayyukan yi
  • Tinubu ya ce katafaren kamfanin na fasahar na da abubuwan da ake bukata da kayan aikin da ake bukata don samar da ayyukan yi a Najeriya
  • Mataimakin shugaban Google, Richard Gingras, ya ce Najeriya na da yawan jama'a da ake bukata domin fitar da sabbin fasahohin zamani

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana shirin gwamnatin Najeriya na aiki da katafaren fasahar Google don samar da ayyukan yi na zamani miliyan daya a kasar.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai baiwa shugaba Tinubu shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Mata 7 Daga Jihohin Katsina, Imo, Abia da Anambra da ke Shirin Zama Ministoci

Legit.ng Hausa ta gano cewa, Tinubu ya yi wannan batu ne a lokacin da mataimakin shugaban kamfanin Google na duniya Richard Gingras ya ziyarci ofishinsa.

Tinubu zai hada kai da Google wajen samawa matasa aiki
Shugaban kasa Tinubu kan ayyukan matasaa Google | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Al'ummar Najeriya na da hazakar juya akalar fasahar zamani

Shugaban ya shaidawa jami’in na Google cewa Najeriya tana da hazikan matasa masu fikira da ke shirye kumake hankoron koyo, musamman a wannan zamani na fasaha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce Google na da iyawa, kayan aiki, da gogewar da matasan Najeriya ke bukata don daura su a hanyar ciyar fa duniyar fasaha gaba.

Tinubu ya ce:

"Na yi farin ciki da cewa Google a shirye yake ya yi hadin gwiwa da mu. Kun amsa kiran da muka yi kan kirkire-kirkire na zamani da kuma taimaka wa matasanmu. Kuna goyon bayan kokarinmu na bunkasa tattalin arzikinzamani.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Ali Nuhu Ya Taya Al'ummar Nijar Alhinin Halin Da Suke Ciki

“A shirye muke mu yi aiki tare da ku kan kudurin da kuka yi na kirkirar ayyukan zamani miliyan 1 a Najeriya.
"Za mu ba ku dukkan goyon bayan da kuke bukata don sauke alhaki na kamfanoni mai fa'ida. Mun fara sauye-sauye a fannin tattalin arzikinmu, duk da cewa yana da wahala.”

Yadda aiki a kasar Landan ke ba mutane kudi

A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar Najeriya da ke zama a Birtaniya, Ihemeson Akunna, ta bayyana yawan kudin da take samu a matsayin mai aikin kula da mutum a kasar.

Ta wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok, tana mai bayyana yadda ake biyanta a kullun saboda yin wannan aiki.

A cewarta, tana samun fam 100 (N56,163) a kullun kan wannan aiki, kuma tana matukar alfahari da neman ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel