Gwamnatin Tarayya Na Tattaunawa Da NLC Kan Tallafin Kudade Na Tinubu Bayan Cire Tallafin Mai

Gwamnatin Tarayya Na Tattaunawa Da NLC Kan Tallafin Kudade Na Tinubu Bayan Cire Tallafin Mai

  • Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da kungiyar NLC don shawo kan wasu matsaloli da suka shafi tallafin kudade
  • Shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila shi ne ke jagorantar ganawar da wasu wakilan kungiyar kwadago
  • Kungiyar Kwadago, NLC ta shirya shiga yajin aiki tare da yin zanga-zanga a gobe Laraba 2 ga watan Agusta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kwamitin ba da tallafi na shugaban kasa ta dage zamanta a jiya Litinin 31 ga watan Yuli zuwa yau Talata 1 ga watan Agusta a fadar shugaban kasa.

Kwamitin shugaban kasan ya kunshi wakilai da dama yayin da kungiyar NLC ta bukaci daga zaman zuwa yau don ba wa mambobinsu damar halartar taron, Legit.ng ta tattaro.

Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da kungiyar NLC kan batun kudaden rage radadin tallafi
Wakilan Gwamnatin Tarayya Na Tattaunawa Da Kungiyar NLC Kan Tallafin Kudade Na Tinubu. Hoto: @saamaccido_/Twitter.
Asali: Twitter

Kungiyar Kwadago ta NLC na shirin shiga yajin aiki a gobe Laraba 2 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin rarraba kudaden tallafi

Kungiyar Kwadago ta nemi Gwamnatin Tarayya ta samar da tallafin da zai rage radadin cire tallafi da Tinubu ya yi a watan Mayu, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin za su tabbatar da kudaden rage radadin na Tinubu sun wadaci ma’aikata don rage musu radadin cire tallafin mai da ya jefa mutane cikin wani hali.

Yayin fara gabatar da ganawar, shugaban NLC, Joe Ajaero bai samu halartar taron ba inda ya bar shugaban kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, Festus Osifo ya jagoranci zaman.

Ganawar da ke gudana a dakin taro na shugaban ma'akata, Femi Gbajabiamila, na jiran bahasi daga kwamitocin sufuri da kuma motoci masu amfani da Gas.

Daga cikin mahalarta taron da ke gunada da kungiyar NLC

A cikin ganawar har ila yau, za a duba yiyuwar dakile shirin zanga-zanga da kungiyar NLC ke kokarin yi a gobe Laraba 2 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Sifetan 'Yan Sanda Ya Tura Muhimmin Sako Ga NLC Da TUC, Ya Ba Su Shawara

Daga wakilan Gwamnatin Tarayya akwai shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila da sakataren din-din-din na ma'aikatar ayyuka, Kachollom Daju sai kuma mai ba da shawara na musamman ga Tinubu a harkar lantarki, Olu Verheijin.

Sauran sun hada da shugaban kamfanin mai NNPCL, Mele Kyari da kuma daraktan kasafi, Ben Akubeze.

Ba Za Mu Amince Da Tashin Hankali Yayin Zanga-Zanga Ba, IGP Ya Fadawa Kungiyoyin Kwadago

A wani labarin, Mukaddashin Sifeta Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya shawarci Kungiyar Kwadago, NLC, kan shirin zanga-zanga a gobe Laraba.

Egbetokun ya ce akwai hanyoyi da dama da ya kamata kungiyar ta bi ba sai dole ta hanyar zanga-zanga ba musamman a irin wannan lokaci da ake ciki.

Ya yi kira ga jami'an 'yan sanda da su tabbatar da doka a kasar da kuma samar da zaman lafiya da kare rayukan al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel