Gwamnan Bauchi Ya Rushe Shugabannin Riko Na Kananan Hukumomin Jihar

Gwamnan Bauchi Ya Rushe Shugabannin Riko Na Kananan Hukumomin Jihar

  • Gwamna Bala Mohammed ya sanar da rushe shugabannin riko na kananan hukumomin jihar baki daya
  • Sanarwar ta fito ne ta hannun sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Kashim a ranar Talata 18 ga watan Yuli
  • Gwamnan ya bayyana cewa an dakatar da shugabannin rikon ne sakamakon karewar da wa’adin mulkinsu ya yi

Bauchi - Gwamnan Bala Abdulkadir Mohammed, ya sanar da rushe dukkanin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar Bauchi ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnan ya ce an dauki matakin na rushe shugabannin ne sakamakon karewa da wa’adin mulkinsu ya yi kamar yadda Leadership ta yi rahoto.

Sanarwar ta fito ne ranar Talata 18 ga watan Yuli, ta hannun sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Muhammad Kashim, wacce ya rabawa manema labarai a Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya rushe shugabannin riko na kananan hukumomin jihar Bauchi
Bala Mohammed ya sauke duka shugabannin riko na kananan hukumomin jihar Bauchi. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Zulum Ya Sanya Magidanta 13,000 Farin Ciki a Jihar Borno Yayin Da Ya Yi Musu Gagarumar Kyauta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An umarci su mika mulki ga shugabannin gudanarwa na kananan hukumominsu

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an umarci shugabannin da aka sauke da su mika ragamar mulki ga shugabannin gudanarwa na kananan hukumominsu.

Ta kara da cewa shugabannin gudanarwar ne za su ci gaba da rike kananan hukumomin har zuwa lokacin da za a nada sababbin shugabannin riko.

Bala Mohammed ya kuma yi wa daukacin shugabannin na riko da aka sauke fatan samun nasara a ayyukansu na gaba tare da gode musu bisa gudummar da suka bai wa jihar.

Bala Mohammed ya yi wa alhazan jihar Bauchi gagarumar kyauta a Saudiyya

Legit.ng ta yi wani rahoto kan gagarumar kyautar da Gwamnan Bala Abdulkadir Mohammed ya yi wa ‘yan jihar Bauchi a kasa mai tsarki.

Gwamnan ya ba da kyauta ta kudade da suka kai Riyal 300, ga kowane daga sama da alhazan jihar 3,000 da suka sauke farali a bana.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Farfesa Njodi a Matsayin SSG, Ya Kaddamar Da Kwamitin Masu Ba Shi Shawara

Gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin ragewa alhazan jihar wani abu daga cikin kudaden da suka kashe yayin aikin hajjin.

An amince da amfani da harshen Hausa a zauren Majalisar Dokokin jihar Bauchi

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan amincewa da Majalisar Dokokin jihar Bauchi ta yi na amfani da harshen Hausa wajen gudanar da al’amuranta.

Kakakin majalisar jihar ta Bauchi Honarabul Abubakar Y Suleiman ne ya bayyana hakan a yayin wani zama da majalisar ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel