Majalisa Ta 10: Tinubu, APC Da Wasu Dalilai 3 Da Ka Iya Sa Akpabio Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Majalisa Ta 10: Tinubu, APC Da Wasu Dalilai 3 Da Ka Iya Sa Akpabio Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

  • Nan da yan awanni kadan yan Najeriya za su san wanda zai zama shugaban majalisar dattawa na gaba
  • Za a rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni sannan a fara sabon zauren majalisa
  • Sai dai, Sanata Godswill Akpabio ne kowa ke ganin zai yi nasarar zama shugaban majalisar dattawa na gaba

A siyasar Najeriya, wasu mutane kan kasance da kwarjini, gogewa, da dabaru na musamman wanda ke sa su zama kan gaba a harkar.

Daya daga cikin irin wadannan mutane da ke haskawa shine Sanata Godswill Akpabio, gogaggen dan siyasa wanda ya yi fice a fagen.

Godswill Akpabio
Majalisa Ta 10: Tinubu, APC Da Wasu Dalilai 3 Da Ka Iya Sa Akpabio Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

A wannan zauren, Legit.ng za ta jero wasu dalilai da ka iya sa Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba.

1. Akpabio ne dan takarar da APC ta tsayar

Kara karanta wannan

Bayan Doke Yari, Sanata Akpabio Ya Karɓi Rantsuwa, Ya Kama Aiki Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

A farkon watan Mayu, kwamitin aiki na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu ta ayyana Sanata Godswill Akpabio a matsayin dan takarar da jam'iyyar ta tsayar ya zama shugaban majalisar dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan goyon baya ya ba Akpabio samun gagarumin karfi domin dai APC ce ke da mafi rinjayen kujeru a majalisar dattawan.

2. Goyon bayan Shugaban kasa Bola Tinubu

Wanene ba zai so samun goyon bayan babban kwamandan rundunar sojoji ba? Lamuncewa Sanata Akpabio da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ya kara sanya shi a gaba.

Sanata mai wakiltan Borno ta kudu, Ali Ndume ne ya yi karin haske kan lamuncewa Sanata Akpabio da shugaban kasa Tinubu ya yi.

A wata hira da Sanata Ndume, ya ce:

"Shugaban kasar ya fada mani dan takarar da ya fi so shine Akpabio kuma cewa na jagorancin kamfen din."

Kara karanta wannan

Godswill Akpabio Ya Doke Abdulaziz Yari, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

3. Goyon baya daga zababbun sanatoci 75

Sanata Ali Ndume ne ya sake bayyana wannan.

A hirarsa na baya-baya, ya bayyana cewa zababbun sanatoci 75 ne suka hade da tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom.

4. Goyon bayan gwamnonin APC

Goyon bayan da Sanata Godswill Akpabio ya samu daga gwamnonin APC ya sake ba shi kafar dama wajen zama shugaban majalisar dattawa na gaba.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya tabbatar da haka.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto, Ganduje ya ce:

"Shugaban majalisar dattawa Najeriya zai fito ne daga kudu maso kudu kuma babu wani mutum sama da tsohon gwamnan Akwa Ibom, gwamna na musamman, minista na musamman wanda zai zama shugaban majalisar dattawa na musamman."

5. Tsarin karba-karba

A ranar Talata, 16 ga watan Mayu, kwamitin aiki na APC ya gana da zababbun sanatoci da sauran manyan jam'iyya don yanke shawara kan yankin da za a mikawa shugabancin majalisar dattawan.

Kara karanta wannan

Ta Kacame a Majalisar Dattawa Bayan Fara Kaɗa Kuri'a, An Yi Fafatawa Mai Zafi Tsakanin Akpabio da Yari

Bayan tattauna da dama, jam'iyyar ta yanke shawarar mika sa ga yankin kudu maso kudu.

Shugaban majalisar dattawa: Zababbun Sanatoci za su siyar da kuri'unsu $5,000, $10,000 ko fiye da haka

A wani labarin, mun ji cewa yayin da ake shirye-shiryen rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, bayanai sun nuna zababbun sanatoci na kokarin siyar da kuri'unsu ga masu neman takarar shugabancin majalisar.

A majalisar dattawa, yan takara sun fara kokarin zawarcin yan majalisa don marawa kudirinsu na son darewa kujerar shugaban majalisar dattawan baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel