"Ba Zan Kunyata Yan Najeriya Ba," Bola Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

"Ba Zan Kunyata Yan Najeriya Ba," Bola Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

  • Shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin ba zai kunyata 'yan Najeriya ba
  • Tinubu ya bayyana haka a wurin bikin karrama shi da lambar yabon GCFR, ya ce ba zai ci amanar Buhari ba
  • Muhammadu Buhari ya karrama zababben shugaban ƙasa da mataimakinsa kwana 4 gabanin miƙa musu mulki

Abuja - Zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai ci amanar 'yardar da shugaba Muhammadu Buhari da miliyoyin 'yan Najeriya suka masa ba.

Ya kuma jaddada cewa ya fahimci girman lambar gurmamawan da aka karrama shi da ita kuma ya san muhimmancin aikin da ke gabansa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Tinubu da Buhari.
"Ba Zan Kunyata Yan Najeriya Ba," Bola Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Tinubu ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabin amincewa bayan karrama shi da lambar yabo ma fi daraja ta ƙasa, 'National Honour of Grand Commander of the Federal Republic' (GCFR) a Abuja.

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Kalamai Masu Ratsa Zuciya A Taron Bankwana

Channels tv ta rahoto Tinubu na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Na fahimci girman wannan karramawa da ka mun yau da kuma girman aikin da ke tunkaro ni. 'Yan Najeriya sun cancanci fiye da haka. Buhari ya tsara mun hanya kuma ba zan yarda na ba shi kunya ba."

Karramawar da aka yi wa zababben shugaban ƙasa ranar Alhamis, 25 ga watam Mayu, ta sanya ya zama mutum na 16 da suka karɓi lambar yabon GCFR a tarihin Najeriya.

Waɗanda suka gabace shi sun ƙunshi Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo, Shehu Shagari, Olusegun Obasanjo, Abdulsalami Abubakar, Ibrahim Babangida, Ernest Shonekan, Sani Abacha Moshood Abiola, Umaru Yar’Adua da Goodluck Jonathan.

Sauran manyan mutanen da Najeriya ta taɓa karramawa da GCFR sun haɗa da, marigayya Saraunuyar Ingila, Queen Elizabeth II, Nelson Mandela (Afirka ta Kudu), da tsohon shugaban Libya, Muammar Gaddafi.

Kara karanta wannan

Shin Buhari Ya Canja Tunani Zai Zauna a Abuja Ya Taimaka Wa Tinubu? Ya Faɗi Gaskiya da Bakinsa

Buhari ya karrama Kashim Shettima

Bayan Tinubu, shugaban ƙasa Buhari ya karrama zababben mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da lambar girma mai daraja ta biyu, Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).

Tun da fari, Buhari ya miƙa wa shugaba mai jiran gado muhimman takardu kamar yadda kundin dokokin zartarwa ya tanada.

Buhari ya yi bankwana da Ministoci

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya ce a shirye yake ya tarbi duk wanda zai iya kai masa ziyara idan har Daura, jihar Katsina ba ta masa nisa ba.

Shugaban ƙasa mai barin gado ya ce idan ya bar mulki zai samu damar yin abubuwa da dama, waɗanda bai samu ikon gudanarwa ba tun watan Mayu, 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel