Dan Takarar Gwamnan PDP a Ogun Ya Shiga Tasku, 'Yan Sanda Na Tuhumarsa Da Siyan Kuri'a Da N2bn

Dan Takarar Gwamnan PDP a Ogun Ya Shiga Tasku, 'Yan Sanda Na Tuhumarsa Da Siyan Kuri'a Da N2bn

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta zargi ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Ladi Adebutu da bayar da cin hanci
  • An zargi Adebutu da loda kuɗi har N10,000 a katikan ATM masu yawa, sannan ya rabawa masu kaɗa kuri’a a jihar Ogun
  • Yanzu haka dai jami’an ‘yan sanda na gudanar da bincike kan lamarin, a yayin da ake kyautata zaton ɗan takarar na PDP ya tsere daga Najeriya

Abeokuta, jihar Ogun Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Ladi Adebutu ya faɗa cikin tashin hankali bayan da ‘yan sanda suka bankaɗo wani shiri na siyan kuri’u na Naira biliyan biyu (2bn).

Idan dai za a iya tunawa, Adebutu ya bayyana a makon da ya gabata cewa ya gudu daga Najeriya ne bisa barazana da rayuwarsa da ya ce ana yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe

Sai dai a yanzu ta bayyana cewa ana tuhumarsa ne da laifin sayen kuri’u da maƙudan kuɗaɗe a babban zaben 2023 da ya gabata.

Adebutu
'Yan sanda sun ce har yanzu Ladi Adebutu bai amsa gayyatar da aka yi masa ba kan zargin sayen kuri’u. Hoto: @ladiadebutu, Prince Dr. Dapo Abiodun - MFR
Asali: Twitter

Adebutu dai shi ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Ogun, wanda ya sha kaye a hannun gwamna mai ci Dapo Abiodun na jam’iyyar APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an ‘yan sanda sun ce Adebutu ya ware kuɗaɗe N2bn domin bai wa masu kaɗa kuri’a cin hanci domin su kaɗa masa kuri’a a zaben na watan Maris.

A cewar jaridar Premium Times a wani rahoto da ta buga a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu, zargin yana kunshe ne a cikin rahoton binciken da ‘yan sandan suka gudanar a kan wata takarda.

Takardar dai ta wasiƙar ƙorafi ce da shugaban jam'iyyar APC na jihar Ogun, Abdullahi Sanusi ya rubutawa babban sufeton ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba.

Kara karanta wannan

Ana Binciken ‘Dan Takaran Gwamnan da Ya Kashe N2bn Ya Saye Kuri’u a Zaben 2023

Abdullahi ya yi ikirarin cewa Adebutu ya raba katinan cirar kuɗi wato ATM ɗauke da lodin N10,000 da aka yi masa, domin jawo hankalin masu kaɗa kuri’a su zaɓe shi a ranar zabe.

Adebutu ya mayar da martani kan zargin

Duk da Adebutu bai amsa gayyatar da ‘yan sanda suka yi masa na yin magana a kan zargin ba, amma kakakinsa Afolabi Orekoya ya musanta zargin, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Tuni dai PDP ta shigar da ƙara a kotun zabe domin kalubalantar nasarar da APC ta samu, don haka Orekoya ya ce ubangidan nasa ya jajirce ne kawai don ganin ya kwato hakkinsa.

A cewar Orekoya, katin ATM din da ‘yan sanda suke magana akai, an bayar da su ne don karfafawa talakawa, ba domin siyan ƙuri’a ba.

'Yan siyasa da batun siyan kuri'u a Najeriya

Siyasar kuɗi ta zama ruwan dare a Najeriya, wanda ya samo asali daga ƙangin talauci, rashin tausayi, da kuma yadda jam'iyyu ke gasa a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Babban Jigo a PDP, Bode George, Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a 29 Ga Mayu

Siyan kuri'a da sayar da kuri'a sun yi daidai da siyar da jam'iyyun siyasa kan abin duniya.

Domin magance yawaitar barazanar siyan kuri'u, an tanadi hukunci a cikin dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.

Laifin dai an tanadar masa hukuncin tarar N500,000 ko daurin watanni 12 ko kuma duka biyun.

APC ta dakatar da wasu manyan 'ya'yanta a Kogi

A wani labarin na daban, jam'iyyar APC ta dakatar da wasu jiga-jigai a jihar Kogi bisa tuhumarsu da laifin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

Jam'iyyar ta zargi wasu daga cikinsu da yin amfani da kuɗaɗe domin kawo mata cikas duk da cewa ana tunkarar zaɓen gwamna a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel