Jam'iyyar APC a Jihar Kogi ta Dakatar Da Shugabanninta Na Wata Karamar Hukuma

Jam'iyyar APC a Jihar Kogi ta Dakatar Da Shugabanninta Na Wata Karamar Hukuma

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi, ta dakatar da dukkanin shugabanninta a ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu
  • Jam'iyyar ta dakatar da shugabanin ne bisa zargin su da yi mata zagon ƙasa domin ganin ƙarfinta ya ragu a jihar
  • Jam'iyyar ta ja kunnen su da su daina kiran kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar na ƙaramar hukumar

Jihar Kogi - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi ta dakatar da dukkanin shugabanninta a mazaɓun ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu, bisa zargin cin dunduniyar jam'iyyar.

Jam'iyyar ta zargi dakatattun shugabannin da yin amfani da kuɗi domin rage mata ƙarfi a jihar, cewar rahoton The Punch.

Jam'iyyar APC ta kori wasu jiga-jiganta a jihar Kogi
Jam'iyyar APC ta dakatar da shugabanninta na karamar hukumar Igalamela/Odolu a jihar Kogi Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da sakataren jam'iyyar APC na jihar, Joshua Onoja, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa jam'iyyar na bincikar dakatattun shugabannin.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Babban Jigon Jam'iyyar APC Ya Fice Daga Jam'iyyar Ana Dab Da Rantsar Da Tinubu

Onoja ya yi bayanin cewa dakatarwar ta su, ta biyo bayan rahotannin yi wa kundin tsarin mulkin jam'iyyar karan tsaye ne, da shugabannin suka yi a mazaɓun da kuma ƙaramar hukumar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar za ta kafa kwamitin riƙon ƙwarya

Sakataren ya kuma bayyana cewa za a kafa kwamitin riƙon ƙwarya da gaggawa, domin ci gaba da kula harkokin jam'iyyar a ƙaramar hukumar, har zuwa lokacin da kwamitin bincike zai kawo rahotonsa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ya umurci dakatattun shugabannin da su mayar da dukkanin kayayyakin jam'iyyar da ke a hannunsu a sakatariyar jam'iyyar ta jiha da ke a birnin Lokoja.

Ya kuma gargaɗe su da kada su ƙara kiran kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar.

Da ya ke mayar da martani kan hukuncin da aka yi musu, ɗaya daga cikin shugabannin da aka dakatar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, sun yi mamakin wannan hukuncin da jam'iyyar ta zartar a kansu.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Halascin Takarar Zababɓen Gwamna da Wasu 'Yan Takara a Jihohin Kano da Abiya

Gwamna Wike Ya Bayar Da Shawara Kan Shugabancin Majalisa

A wani labarin na daban kuma, gwamna Wike ya bayyana matasayarsa kan shugabancin majalisa ta 10.

Gwamnan ya shawarci masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai, da su mutunta tsarin da jam'iyyar APC da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, suka zo da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng