Yanzu-Yanzu: Kotun Zabe Ta Yi Fatali Da Wata Bukatar Atiku da Peter Obi

Yanzu-Yanzu: Kotun Zabe Ta Yi Fatali Da Wata Bukatar Atiku da Peter Obi

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta sanya ƙafa ta yi fatali da buƙatar a riƙa haska zamanta kai tsaye a talbijin
  • Atiku Abubakar da Peter Obi ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun PDP da LP ne suka shigar da ƙorafin a gaban kotun zaɓen
  • Kotun ta yanke hukunci cewa wannan ƙorafin na su bai cancanta ba saboda haka ba za ta amince da shi ba

Abuja - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ta yi fatali da buƙatar a haska zaman kotun kai tsaye, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Shugaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasar, mai shari'a Haruna Tsammani, shine ya yi fatali da buƙatar haska zaman kotun kai tsaye.

Kotun zabe ta yi fatali da bukatar haske zamanta kai tsaye
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa Hoto: Gazettengr.com
Asali: UGC

A zaman kotun na ranar Litinin, mai shari'a Haruna Tsammani, ya bayyana cewa ƙorafin na jam'iyyar PDP da Labour Party, bai cancanta ba, cewar rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kungiyar ASUU Ta Zabi Sabon Shugabanta Na Kasa

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, su ne suka shigar da wannan buƙatar, wacce zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na jam'iyyar APC, ya ke jayayya da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shigar da ƙorafi a ranar 8 ga watan Mayun 2023, inda ya buƙaci kotun da ta riƙa haska zamanta na kowace rana kai tsaye, a ƙarar da ya shigar ta ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu.

Sai dai, sati ɗaya bayan shigar da ƙorafin, Bola Tinubu, ya yi jayayya da buƙatar a riƙa haska zaman kotun kai tsaye, inda ya bayyana shi a matsayin yin karantsaye ga kotun.

Kotun Koli Ta Tsaida Ranar Sauraron Shari’ar PDP v Tinubu da Shettima

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Babban Jigon Jam'iyyar APC Ya Fice Daga Jam'iyyar Ana Dab Da Rantsar Da Tinubu

A wano rahoton na daban kuma, kotun ƙoli ta tsayar da ranar da za ta yanke hukuncin kan ƙarar da jam'iyyar PDP ta shigar da Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Jam'iyyar PDP dai ta garzaya kotun ne, tana neman a rushe takarar Bola Tinubu da Ƙashim Shettima na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Asali: Legit.ng

Online view pixel