Da Dumi-Dumi: Kungiyar ASUU Ta Sake Zaben Farfesa Emmanuel Osodoke a Matsayin Sabon Shugaba

Da Dumi-Dumi: Kungiyar ASUU Ta Sake Zaben Farfesa Emmanuel Osodoke a Matsayin Sabon Shugaba

  • Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta sake zaɓar Farfesa Emmanuel Osodoke, a matsayin shugabanta na ƙasa
  • Farfesa Emmanuel Osodoke ya sake ɗarewa kan kujerar shugabancin ƙungiyar ba tare da wani ya nemi kujerarsa ba
  • Ƙungiyar ta sake mayar da Osodoke kan kujerarsa da wasu shugabanninta ne, a zaɓen da ta gudanar a jami'ar Jos

Jos, Plateau - Mambobin ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU), da safiyar ranar Litinin sun sake zaɓar Farfesa Emmanuel Osodeke, a matsayin sabon shugaban ƙungiyar wanda zai sake jan ragamarta na wasu shekara biyu masu zuwa.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa, Osodoke ya lashe zaɓen ne ba tare da wani abokin hamayya ba.

ASUU ta sake zabar Farfesa Osodoke a matsayin shugabanta
Farfesa Emmanuel Osodoke, shugaban kungiyar ASUU Hoto: Dailypost.com
Asali: UGC

Bayan Farfesa Osodoke wanda ya fito daga jami'ar Michael Okpara University of Agriculture, Umudike, jihar Abia, mambobon ƙungiyar sun sake zaɓar Chris Piwuna, na kwalejin lafiya a jami'ar Jos, a matsayin mataimakin shugaba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Zabe Ta Yi Fatali Da Wata Bukatar Atiku da Peter Obi

An sake zaɓar shugabannin ne a lokacin taron deliget ɗin ƙungiyar na ƙasa karo na 22, wanda aka gudanar a jami'ar Jos, a tsakanin ranakun 19 da 21 ga watan Mayun 2023, cewar rahoton The Cable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran shugabannin da aka zaɓa

Sauran shugabannin ƙungiyar na ƙasa da aka sake zaɓa a wajen taron sun haɗa da, Farfesa Siji Sowande (Ma'aji), Farfesa Ade Adejumo (sakataren kuɗi), Dr Austen Sado (sakataren zuba jari) Dr Adamu Babayo (mai binciken kuɗi) da Dr Aisha Bawa wacce ta maye gurbin Dr Stella-Maris Okey a kujerar sakataren walwala.

Osodeke wanda ya tattauna da wakilin majiyar mu, akan hanyarsa ta zuwa birnin tarayya Abuja bayan an kammala taron, ya bayyana taron a matsayin wanda ya gudana cikin nasara.

A kalamansa:

"Mun kammala taron deliget ɗin mu na ƙasa a birnin Jos. Muna kan hanyar komawa birnin tarayya Abuja. Za mu fitar da sanarwa kan taron da sake zaɓe na da aka yi da sauran shugabannin ƙungiyar na ƙasa, idan mu ka koma ofishin mu. Nagode."

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Bayyana Gaskiya Dangane Da Soke Halascin Takarar Zababben Gwamnan Jihar Abia

Gwamnatin Tarayya ta Tsokano Fada, An yi wa Ma’aikata Karin Albashi, An Ware jami’o’i

A baya rahoto ya zo kan yadda ƙungiyar ASUU ta ke shirin sanya ƙafar wando ɗaya da gwamnatin tarayya kan ƙarin albashi.

Gwamnatin tarayya ta biya ma'aikata ƙarin albashi amma ta ware malaman jami'o'i, wanda hakan ya fusata malaman na jami'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel