‘Yan PDP, NNPP Sun Ayyana Matsaya a Majalisa Ganin Jam’iyyar APC Ta Yi Kason Kujeru

‘Yan PDP, NNPP Sun Ayyana Matsaya a Majalisa Ganin Jam’iyyar APC Ta Yi Kason Kujeru

  • Wata kungiya ta ‘yan majalisa za ta goyi bayan matakin da APC ta dauka wajen kason kujeru
  • Bayan yin na’am da matsayar da APC NWC ta cin ma, ‘yan siyasar za su ba Bola Tinubu hadin-kai
  • Usman Bello Kumo (APC), Hon. Kingsley Chinda (PDP), Aliyu Sani Madaki (NNPP) su ka shaida haka

Abuja - Wata kungiya ta gamayyar ‘yan majalisar tarayya ta rungumi matsayar da jam’iyyar APC NWC ta dauka na ware wadanda za su rike shugabanci.

This Day ta rahoto cewa ‘Yan siyasar da suka hada da zababbun ‘yan majalisa da wadanda suka zarce kan kujerunsu, sun nuna za su yi biyayya ga APC.

Kungiyar nan ta kunshi ‘ya ‘yan APC mai rinjaye da kuma sauran jam’iyyun hamayya da ke da wakilci a majalisar wakilan tarayya da za a rantsar.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigan 'Yan Majalisa 5 Na APC Da Suka Lashi Takobin Yaƙar Ɗan Takarar Tinubu a Majalisa Ta 10

Jam’iyyar APC
Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

An fitar da jawabin hadaka

Shugabannin kungiyar; Usman Bello Kumo, Kingsley Chinda da sakatarensu, Aliyu Sani Madaki suka tabbatar da wannan a takardar da suka fitar a jiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Ya ‘yan APC, PDP da NNPP a majalisar sun sha alwashi za su yi aiki da gwamnati mai zuwa.

Takardar da ta samu sa hannun wakilan jam’iyyun nan, ta nuna sauran takwarorinsu da abokan aiki za su goyi bayan APC mai-rinjaye sau da kafa.

"A matsayin kungiya, gungunmu a majalisa ta 10 ta yi na'am da yadda aka tsara kason mukamai a jam'iyyar APC.
Mun yi amanna da bin tsarin damukaradiyya yadda yake a ko ina a Duniya, shiyasa mu ke so mu hada kai a matsayin ‘yan majalisa, ayi aiki da kowa.
Mu na so mu yi aiki tare da sauran bangarori musamman masu zartarwa, ba tare da mun yi watsi da damar cin gashin kanmu da muke da shi a doka ba.

Kara karanta wannan

Lauyan Abba Gida-Gida Ya Yi Maganar Yiwuwar Samun Nasarar APC da Gawuna a Kotu

- Hon. Usman Bello Kumo, Hon. Kingsley Chinda, Aliyu Sani Madaki

Kowa ya bi?

Rahoton ya ce tun da APC NWC ta tsaida magana, Kumo, Chinda da Madaki a madadin sauran mutanensu sun yi na’am da duk matakin da aka dauka.

Bayan alkawarin ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu hadin-kai, ‘yan siyasar sun nuna a shirye suke wajen aiki da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen majalisa.

Zancen teburin mai shayi

A ranar Laraba, Legit.ng Hausa ta tattauna da Lauyan da ya ke kare NNPP, ya shaida mana za a kori karar APC domin jam’iyyar ba da muhallin nasara.

Barista Tudun Wazirci ya ce nasara ta jam’iyyar NNPP da Kanawa ce, ya ce batun an gano takardun kuri’u marasa hatimi, zancen teburin mai shayi ne.

Lauyan ya ce a korafin da APC ta ke yi, babu inda ta kawo maganar amfani da takardun kuri’u na bogi, amma ana fadan haka ne saboda yaudara.

Kara karanta wannan

Za Mu Yi Amfani da Rudanin APC, Mu Tsaida Shugabannin Majalisa Inji Sauran Jam’iyyu

A cewar Lauyar, tun da masu kara ba su hada da Nasiru Gawuna a cikin shari’ar ba, babu yadda za a ba ‘dan takaran APC nasara ko da shi ne da gaskiya.

Menene dalilin fifita Arewa maso yamma?

An rahoto Dr. Tajuddeen Abbas yana cewa Arewa maso yamma na dauke da jihohi 7, a zaben da ya gabata a Fubrairu, sun ba Bola Tinubu kuri’u miliyan 2.65.

Mutane 93 a cikin 360 da ake da su a majalisar tarayya sun fito daga yankin ne, ganin su ke da kusan 26% na kujeru, Abbas ya ce ya kamata ayi la’akari da haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel