Biloniyoyin 'yan siyasa 10 a Najeriya da kiyasin kudinsu

Biloniyoyin 'yan siyasa 10 a Najeriya da kiyasin kudinsu

Duk da kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashen da talauci ya yi wa katutu, Najeriya ta kunshi attajiran 'yan siyasa masu kazamin kudi ko a idoon duniya.

Ba boyayyen abu bane cewa wasu 'yan tsirarun tsofin shugabanni da shugabanni masu ci a yanzu sun mallaki dukiyar da zata iya wadata kasa baki daya.

Duk da kokarin irin wadannan shugabanni wajen boye irin kadarori da dukiyar da suka mallaka, hakan bai hana wasu kafafen watsa labarai irinsu Forbes da saransu su bankado irin makudan kudin da 'yan siyasar suka mallaka ba. 'Yan siyasar da suke mataki na 1 da na 2 sun mallaki jimillar kudin da suka zarce jimillar kudin shigar jihohin Yobe, Gombe da Ebonyi.

10. Rotimi Amaechi

Amaechi, kamar yadda aka fi kiransa, ssohon shugaban majalisar dokokin jihar Ribas ne kafin daga bisani ya zama gwamna a jihar, kuma yanzu haka shine ministan sufuri na kasa.

Dan siyasar ya mallaki kadarori da motocin alfarma da suka hada Mercedes Maybach Vision 6, Mercedes AMG G63, Mercedes S550, Land Rover Discovery, Lexus LX 570 da sauransu. Ana zargin cewa ya mallaki jirgin sama na kashin kansa, wanda aka yi kiyasin cewa kudinsa ya kai biliyan N8.8, amma dan siyasar ya musanta hakan.

An yi kiyasin cewa ya mallakia kudin da suka tasamma biliyan N282.

9. Dino Melaye

Kwanan nan aka kayar da Dino Melaye a zaben kujerar sanatn jihr Kogi ta yamma da kotu ta rushe kuma ta bayar da umarnin a sake gudanar da shi.

Sanata Smart Adeyemi, na jam'iyyar APC, ne ya kayar da Dino Melaye a zaben da ak sake gudanar wa ranar 16 ga watan Nuwamba, sannan aka kammala shi ranar 30 ga wata.

Melaye ya yi suna wajen nuna irin tarin motocin kece raini da alfarma da ya mallaka, wanda suk hada da; Bugatti Veyron, wacce kudinta ya kama miliyan N616, Roll Royce guda uku da jimillar kudinsu ya kama miliyan N318, Lamborghini Huracan da kudinta ya kama N86.7, Bentley Continental da kudinta ya kama miliyan N71 da sauran wasu motoci da yawa da za a iya bayyana sayensu a matsayin almubazzaranci.

An yi kiyasin cewa Melaye ya mallaki adadin kudin da yawansu ya kai biliyan N290.

8. Alhaji Ahmadu Adamu Mu'azu

Tsohon gwamna ne a jihar Bauchi daga shekarar 1999 zuwa 2007 kafin daga bisani ya zama shugaban jam'iyyar PDP na kasa a shekarar 2013.

Hukumar EFCC ta taba kwace wani gidan mallakar Mu'azu da ke yankin Ikoyi a jihar Legas, inda har ta samu makudan kudin da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan $50 a boye a cikin wasu asusu na musamman ba wuta bata cinsu.

Duk da kamfanin da ya yi kwangilar gina gidan ya bayyana cewa gidan mallakar Mu'azu ne, tsohon gwamnan ya musanta hakan tare da bayyana cewa ana kokarin bata masa suna ne kawai.

An yi kiyasin cewa tsohon gwamnan ya mallaki kudin da yawansu ya kai biliyan N282.

7. Orji Uzor Kalu

A cikin makon da muka yi bankwana da shi ne wata kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Legas ta yanke wa tsohon gwamna kuma Sanata mai ci, Orji Uzor Kalu, hukuncin daurin shekaru goma sha biyu a gidan yari bayan samunsa da laifin karkatar da fiye da biliyan N7 daga asusun gwamnatin jihar Abiya.

Yana da hannun jari a kungiyar kwallon kafa mafi karfi a Najeriya, Enyimba FC, sannan ya mallaki wani katafaren gida mai dakuna 400 da aka yi kiyasin cewa kudinsa ya kai biliyoyi.

An yi kiyasin cewa tsohon gwamnan ya mallaki kudin da yawansu ya kai biliyan N470.

6. Atiku Abubakar

Ba ya bukatar wata gabatar wa a wurin duk wani dan Najeriya. Sau uku Atiku yana takarar kujerar shugaban kasa amma bai taba samun nasara ba.

Atiku dan siyasa ne, dan kasuwa, kuma daya daga cikin attajirai da ke tallafa wa talaka wa da masu karamin karfi.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya mallaki wani jirgin sama, 'Phenom 100', wanda aka yi kiyasin cewa kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan $4.1, sannan ya mallaki wani katafaren gida na dalar Amurka miliyan $2.95 a yankin Potomac da ke jihar Maryland, kasar Amurka.

Kazalika, ya mallaki wata jami'a mai zaman kanta da ake kira AUN (American University of Nigeria), wacce ya kafa a shekarar 2004.

An yi kiyasin cewa ya mallaki kudin da yawansu ya kai biliyan N470.

5. Rochas Okorocha

Tun bayan saukarsa daga kan kujerar gwamna a jihar Imo, hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta fara binciken tsohon gwamna Rochas Okorocha, wanda yanzu haka sanata ne mai wakiltar jihar Imo ta yamma a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Rochas ya kasance mashahurin dan kasuwa mai nasibi kafin daga bisani ya shiga siyasa. Ya mallaki wata gidauniya da ke gina makarantu domin ilimantar da 'ya'yan talaka wa da masu karamin karfi.

Tsohon gwamnan ya mallaki motocin alfarma da suka hada da da Roll Royce Phantom, Mercedes Benz S600, Mercedes Benz Klassen V220, Mercedes Benz AMG63, Lexus LX 570 da sauransu. Kazalika, Rochas ya yi ikirarin cewa ya mallaki jirginsa na kashin kansa tun kafin ya zama gwamna.

An yi kiyasin cewa ya mallaki kudin da yawansu ya kai biliyan N507.

4. Ifeanyi Ubah

Bayan kasancewarsa shahararren dan kasuwa, yanzu haka Ifeanyi Ubah sanata ne da ke wakiltar jihar Anambra ta kudu a majalisar dattijai. Ya mallaki wani kamfanin harkokin man fetur da ke kira 'Capital Oil', sannan ya mallaki kungiyar kwallon kafa da ake kira 'Ifeanyi Ubah football club'.

Ifeanyi Uba ya mallaki motocin alfarma da suka hada da Roll Royce, Land Rover, Cadillac Escalade, Toyota Land Cruiser da Toyota Highlander, sanna ya mallaki jirgin sama da aka yi kiyasin cewa kudinsa ya kai dalar Amurka $31.

An yi kiyasin cewa ya mallaki kudin da yawansu ya kai biliyan N508.

3. Olusegun Obasanjo

Babbar kadarar Obasanjo da kowa ya sani, ita ce katafariyar gonarsa da ke garin Otta a jihar Ogun. Bayan mallakar daya daga cikin manyan gonaki a nahiyar Afrika, Obasanjo dan kasuwar haka da sayar da man fetur ne.

Obasanjo, tsohon shugaban kasa a mulkin soji da dimokradiyya, ya mallaki karamin jirgin sama da kuma jirgin sama mai saukar ungulu.

An yi kiyasin cewa Obasanjo ya mallaki kudin da yawansu ya kai tiriliyan N1.8.

2. Ibrahim Badamasi Babangida (IBB)

Tsohon soja ne da ya mulki Najeriya daga ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 1985 zuwa ranar 26 ga watan Agusta 1993. Ya rike mukamai da dama a rundunar soji kafin ya zama shugaban kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa IBB ya mallaki wani kamfani, 'Fruitex International', da ke kasar Ingila, sannan ya mallaki kaso 24% na daya daga kamfanonin sadarwa da ke Najeriya, sannan ya mallaki wani jirgi da kudinsa ya zarce naira biliyan daya.

An yi kiyasin cewa ya mallaki kudin da yawansu ya kai tiriliyan N1.8, lamarin da saka shi zama na biyu a jerin 'yan siyasar Najeriya masu kazamin kudi.

1. Bola Tinubu

Daya daga cikin masu burin gadar kujerar shugaban Buhari a shekarar 2023, an fara zabensa a matsayin sanata daga jihar Legas a shekarar 1993 kafin daga bisani a zabe shi a matsayin gwamnan jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007.

A baya hukumar EFCC da ICPC sun fara binciken Tinubu, amma yanzu an jingine duk wani batu na binciken da ake yi masa.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa ana tuhumar Tinubu da hannu a cikin safarar miyagun kwayoyi a kasar Amurka a tsakanin 1988 zuwa 1993.

An dade ana zargin cewa Tinubu ne kadai dan siyasar Najeriya da manyan motocin dakon kudi ke sauke masa kudi a gidansa d ke Ikoyi, jihar Legas.

Ya mallaki wasu manyan motocin alfarma da suka hada da G - Wagon da kudinta ya kai miliyan N600. Mercedez Benz guda biyu, Range Rover, Lexus LX 570 da sauransu, sanna ya mallaki jiragen sama na kashin kansa da suka hada Bombadier Global Express XRS da kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan N60.

An yi kiyasin cewa Tinubu ya mallaki adadin kudin da yawansu ya kai tiriliyan N3.4.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel