Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Osun

Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Osun

  • Kotun ƙoli ta shirya yanke hukunci kan karar da ta shafi tsohon gwamna Gboyega Oyetola da gwamna Ademola Adeleke na Osun
  • Kotun ta sanya ranar Talata 9 ga watan Mayu, 2023 domin yanke hukunci kan korafin zaben gwamnan Osun wanda ya gudana a watan Yuli, 2022
  • Kotun ta cimma wannan matsaya ne bayan sauraron kowane bangare a zaman ranar Litinin 8 ga watan Mayu

Abuja - Rahoton The Nation ya nuna cewa Kotun koli a Najeriya ta shirya yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya shigar gabanta yana kalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke.

Oyetola da Adeleke.
Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Osun Hoto: Gboyega Oyetola, Ademola Adeleke
Asali: UGC

Kotun, wacce ake wa laƙabi da daga ke sai Allah ya isa ta tsara yanke hukunci ranar Talata, 9 ga watan Mayu, 2023, da misalin karfe 2:00 na rana.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunayen Manyan Alƙalai 5 da Zasu Jagorancin Shari"a Kan Zaben Tinubu a 2023

A ƙorafin da ya ɗaukaka, Oyetola ya roki Kotun koli ta rushe hukuncin da Kotun ɗaukaka kara ta yanke ranar 25 ga watan Maris, wanda ya tabbatar da nasarar Adeleke a zaben Osun.

Kotun koli zata yanke makomar Adeleke da Oyetola gobe

Kotun ɗaukaka ƙara ta jingine hukuncin da Kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan Osun ta yanke, wanda ya baiwa Oyetola nasara kuma ta tsige Adeleke.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamitin alkalai 5 na Kotun koli ne ya bayyana lokaci da ranar yanke hukuncin ƙarshe bayan sauraron bayanan kowane ɓangare a zaman yau Litinin.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a ranar 16 ga watan Yuli, 2023, hukumar zabe INEC ta gudanar da zaben gwamnan jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Timothy Owoeye, ya yi zargin cewa wasu shugabannin APC ne suka ware kansu, suka haɗa kai da PDP domin cin amanar tsohon gwamna Oyetola da jam'iyyarsa.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Bola Tinubu

A cewarsa, hakan ne ya yi sanadiyyar rashin nasarar jam'iyyar APC da gwamna Oyetola a zaɓen gwamnan jihar da ya gabata, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

AA ta janye korafin da ta shigar gaban Kotu

A wani labarin kuma Jam'iyyar Action Alliance (AA) Ta Janye Karar da Ta Shigar da Zababben Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu

A ranar fara zaman sauraron karar zaben shugaban ƙasa, jam'iyyar AA ta samu rabuwar kai wanda ya samo asali daga rikicin cikin gida da take fama da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel