Jam'iyyar Action Alliance Ta Janye Karar da Ta Shigar da Bola Tinubu

Jam'iyyar Action Alliance Ta Janye Karar da Ta Shigar da Bola Tinubu

  • Ƙotun sauraron kararrakin da suka danganci zaben shugaban kasa a Najeriya ta fara zama yau Litinin a Abuja
  • Kwamitin alkalai 5 da ke jagorantar zaman ya kori karar da AA ta shigar bayan jam'iyyar ta nemi janyewa
  • Bayn ɗaukar wannan mataki ya rage saura korafe huɗu a gaban Kotu, ta raba zama tsakanin ranar Litinin da Talata

Abuja - Jam'iyyar Action Alliance ta janye ƙorafin da ta shigar gaban Kotu kan zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Channels tv ta rahoto cewa jam'iyyar adawa AA ta sanar da janye korafinta a farkon zaman Kotun sauraron ƙarar zaben shugaban ƙasa na 2023 ranar Litinin a Abuja.

Bola Tinubu.
Jam'iyyar Action Alliance Ta Janye Karar da Ta Shigar da Bola Tinubu Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Sai dai jam'iyyar AA ba ta bayyana ainihin dalilin da ya sa ta ɗauki matakin janya ƙarar da ta shigar da Tinubu ba a ranar zaman farko.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunayen Manyan Alƙalai 5 da Zasu Jagorancin Shari"a Kan Zaben Tinubu a 2023

Kotu ta yi watsi da ƙarar jam'iyyar AA

Nan take Kotun ta kori ƙarar jam'iyyar AA, wacce ta kalubalanci nasarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasan da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Tsammani ya bayyana cewa Kotu ta kori karar ne bisa dogaro da tanadin kundin dokokin zaɓe a Najeriya.

Tun da fari, lauyoyi biyu, Oba Maduabuchi (SAN) da Malachy Nwaekpe Esq suka gabatar da kansu a matsayin waɗanda zasu kare karar jam'iyyar AA.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar AA, David Okonigbuan, ne ya shigar da ƙarar INEC, APC, Bola Tinubu da Hamza Al-Mustapha, gaban Kotu.

Mista Okonigbuan ya kalubalanci waɗanda yake kara kan cire sunansa daga cikin 'yan takarar shugaban ƙasa a zaben da INEC ta ce Tinubu ne ya samu nasara.

Jam'iyyar ta tsayar da Al-Mustapha a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa kuma INEC ta fitar da sunansa a cikin jerin sunayen 'yan takara, kamar yadda Daily Trsut ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Ƙarar Zaɓe: Atiku Ya Buƙaci A Haska Zaman Kotun Kai Tsaye A Talabijin

Waɗanda ake kara basu yi musun janye karar da AA ta yi ba, bisa haka Kotun ta yi fatali da korafin. A halin yanzun saura kararraki huɗu a gaban kwamitin Alƙalai 5.

Jerin sunayen Alƙalai da zasu jagoranci shari'ar su Atiku da Obi

A wani labarin kuma Jerin Manyan Alkalai 5 da Zasu Jagorancin Shari'a Kan Zaben Shugaban Kasa

A yau da misalin karfe 9:15 Kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta fara zamanta a Abuja.

Mun tattaro muku jerin sunayen Alkaln guda 5 waɗanda zasu ja ragamar sauraron korafi kan nasarar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel