Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

  • Jam’iyyar APC ba ta yarda Bala Mohammed ya yi nasara ba, ta ce magudi aka tafka a zaben 2023
  • A jihar Delta, Kwamitin yakin zaben Jam’iyyar APC bai gamsu da nasarar Sheriff Oborevwori ba
  • APC za ta dauki hayar Lauyoyi da nufin kalubalantar sakamakon zaben da Hukumar INEC ta sanar

Delta - Kwamitin yakin neman zaben Gwamnan jihar Delta a APC ta bakin Ima Niboro, ya ki karbar sakamakon da hukumar INEC ta sanar.

Premium Times ta rahoto Ima Niboro yana cewa ba su yarda Sheriff Oborevwori na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben Gwamnan a jihar Delta ba.

Ovie Omo-Agege wanda ya nemi kujerar a jam’iyyar PDP ya zo na biyu da kuri’u 240,229, ‘dan takaran PDP ya ba shi ratar kuri’u 120, 000.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Kwankwadi Giya Saboda Murnar Tambuwal Ya Kunyata a Sokoto

Kwamitin yakin zaben APC ya ce ya na da hujjojin da ke nuna an saba doka a zaben, an hana mutane kada kuri’arsu ga ‘dan takaran da suke so.

An tanadi hujjojin zuwa kotu

Niboro yake cewa su na da tulin hujjoji da ke nuna yadda aka ki yin amfani da na’urar BVAS, aka raba takardun bogi, aka yada sakamakon karya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika an rahoto kwamitin zaben yana zargin ‘yan daba sun rika tada rikici, su na hana magoya bayan jam’iyyar APC kada kuri’a a Delta.

‘Yan Takaran APC
Yakin neman zabe a Bauchi Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Hakan ya jawo a cewarsa, babu mai yin murna da wannan nasara da aka ce PDP ta samu a Delta, a karshe aka yi kira ga magoya baya suyi hakuri.

Ana haka ne sai ga shi abokin takarar Sanata Omo Agege, Sunny Areh yana cewa ba su gamsu da zaben ba, a karshe aka fahimci za su shigar da kara.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

Zaben jihar Bauchi

Wani makamancin rahoton ya nuna jam’iyyar APC ba ta gamsu da zaben Gwamnan jihar Bauchi inda a nan kuma Gwamnan PDP ne ya samu nasara.

Sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka ya fitar da jawabi yana cewa INEC ta binciki yadda aka saba doka wajen zaben Gwamna a Bauchi.

Jaridar ta rahoto Morka yana cewa ba ayi amfani da BVAS yadda ya kamata ba, sannan an tada zaune tsaye saboda Bala Mohammed ya zarce.

Jam’iyyar APC ta ce an yi zabe fiye da kima, an tafka magudi, ‘yan daba sun yi aiki, kuma an hana mutane kada kuri’a duk da nufin PDP ta ci zabe.

Bello Mohammed Matawalle ya sha kasa

Rahoto ya zo cewa Bello Mohammed Matawalle ya fadi zabe a hannun Lawal Dare da ratar kuri'u 65, 000, Gwamnan ba zai koma mulki ba a 2023.

Jam’iyyar PDP ta doke APC a kananan Hukumomi har10; Anka, Bukuyum, Bungudu, Gumi, Gusau, Kaura, Maru, Shinkafi, Tsafe da Zurmi a zaben.

Kara karanta wannan

Binani: Minista Ya Yi Maganar Makarkashiyar da PDP ke Shiryawa a Zaben Adamawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel