Jam'iyyar NNPP Ta Janye Zanga-Zangar Lumana Kan DSS A Kano

Jam'iyyar NNPP Ta Janye Zanga-Zangar Lumana Kan DSS A Kano

  • Jam'iyyar NNPP ta ce ta dakatar da zanga-zangar lumana da za ta gudanar don nuna kin amicewa da daraktan DSS saboda zargin da yan sanda kan kada bata gari su juya akalar zanga-zangar
  • Shugaban jam'iyyar NNPP, Umar Doguwa, ta bakin Abdullahi Baffa Bichi ya ce sun fasa zanga-zangar saboda yadda su ke girmama yan sanda
  • Jam'iyyar ta zargi barin daraktan a matsayin muradin Gwamna Ganduje don musguwa magoya bayan jam'iyyar da kuma taimaka masa wurin magudin zabe

Kano - Jam'iyyar NNPP a Jihar Kano ta dakatar da zanga-zangar da shirya yi don nuna kin jinin daraktan hukumar tsaron farin kaya na Jihar, Mohammed Alhassan wanda su ke zargin dadewarsa a Kano bayan wa'adin aikinsa a jihar ya kare watanni 15 da su ka gabata.

Jam'iyyar ta zargin daraktan DSS din da kulla aminta tsakaninsa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje don sauya alkaluman zaben gwamna da na yan majalisun jihar ga jam'iyya mai mulki, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Ba Wa Yan Siyasa Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Daf Da Zaben Gwamnoni

Jami'an Hukumar DSS
NNPP Ta Janye Zanga-Zangar Lumana Kan DSS A Kano. Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke jawabi a madadin shugaban jam'iyyar, Umar Haruna Doguwa a taron manema labarai, Dr Baffa Abdullahi Bichi, ya ce fasa zanga-zangar ya biyo bayan koken da hukumar yan sanda ta yi cewa su na tsoron ka da bata gari su yi amfani da damar su mayar da zanga-zangar wani abu na daban.

Bichi wanda ya sha kayi a takarar kujerar sanatan Kano ta Arewa a zaben 25 ga watan Fabrairu ya ce, ''Mu ma su son zaman lafiya ne, kuma ba za mu ki jin maganar manya ba.''

Tsohon shugaban hukumar TETFUND din ya ce:

''Matsayar shi ne ba wai don Mal Alhassan ya wuce shekarun aikinsa ba, amma an bar shi a aikin, kuma a Kano saboda bukatar Gwamna Ganduje wadda abokinsa ne tun dadewa, kuma shi ya ke wa aiki.''

Kara karanta wannan

"Ban Janye Wa Kowa Ba", Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar Labour A Kaduna

Bichi ya ce:

''Saboda rokon DIG na shiyya ta daya na rundunar yan sandan Najeriya, kuma saboda yadda mu ke girmama yan sanda, mun yanke shawarar dakatar da zanga-zangar lumana.''

Jigon NNPP ya cigaba da cewa:

"Iya daren jiya yan jam'iyyar mu guda biyar hukumar DSS ta kama ba bisa ka'ida ba a Madobi tare da kai su wajen da ba a bayyana ba.''

Ya jaddada cewa:

''Wannan shi ne aikin da aka bar daraktan hukumar DSS ya yi - ya kama jagororin mu, ya tsorata magoya bayan mu, a takurawa ma su zabar mu, a kuma kirkiri rikici don yin magudin zabe.''

Ya yi kira ga ma su sanye ido daga kasashen waje akan zabe a Kano da su sanya kan hukumar DSS a Kano.

Kusa a jam'iyyar PDP ya yi murabus yan awanni kafin zaben gwamna

A wani rahoton kun ji cewa jigon jam'iyyar PDP a jihar Delta, Cif Dele Omenogor ya fita daga jam'iyyar ana yan awanni zaben gwamna na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Rundunar Yan Sanda Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al’ummar Jihar Kano Ana Gab Da Zabe

Omenogor ya koka da cewa gwamnatin Gwamna Ifeanyi Okowa ta yi watsi da masarautar Amai da daukakin kasar Ukwuani, hakan yasa ya fice daga PDPn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel