Shugabancin Majalisar Tarayya: Zababbun Yan Majalisa Sun Isa Aso Rock Don Ganawa Da Tinubu

Shugabancin Majalisar Tarayya: Zababbun Yan Majalisa Sun Isa Aso Rock Don Ganawa Da Tinubu

  • Za a yi ganawa mai muhimmanci tsakanin zababben shugaban kasa, mataimakinsa da zababbun yan majalisa
  • Bola Tinubu da yan majalisa mai kamawa za su tattauna kan yadda shugabancin majalisa ta 10 zai kasance
  • Manyan jiga-jigan na APC za kuma su tattauna kan yadda zaben gwamnonin jihohi na ranar 18 ga watan Maris za su kasance

Abuja - Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima za su gana da zababbun yan majalisar tarayya na jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Za a yi ganawar ne da yammacin yau Litinin, 13 ga watan Maris a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa tuni zababbun yan majalisar suka isa dakin taro na fadar shugaban kasa suna jiran isowar zababben shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu: Ohanaeze Ta Fadi Wanda Take So Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Wasu daga cikin yan majalisar da suka hallara don ganawa da Bola Tinubu
Shugabancin Majalisar Tarayya: Zababbun Yan Majalisa Sun Isa Aso Rock Don Ganawa Da Tinubu Hoto: Leadership
Asali: UGC

An tattaro cewa dalilin ganawar tasu don tattauna yadda za a raba shugabancin majalisar dokokin tarayya ta 10 ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma tattaro cewa za su tattauna a kan zaben gwamnoni da na yan majalisun jihohi da za a yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Zabbun yan majalisa sun fara hallara

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wasu tsoffin yan majalisa da aka sake zaba da sabbin yan majalisa sun hallara don ganawar.

Yan majalisar sun hada da Sanata Orji Uzor Kalu, Sanata Michael Bamidele, Sanata Mohammed Ali Ndume, Sanata Adeola Olamilekan, Zababben Sanata Abdulaziz Yari, da sauransu.

Ohanaeze ta bukaci a ba Gwamna Umahi shugaban majalisar dattawa na gaba

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar dattawan kudu maso gabas, Ohanaeze Ndigbo sun bukaci da a baiwa gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi mukamin shugaban majalisar dattawa na gaba.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zaben Gwamna: APC Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al'ummar Wata Jihar Kudu

A cewar kungiyar, mikawa Inyamuri wannan kujera shine zai wanke zargin da yankin ke yi na cewa an mayar da ita saniyar ware kuma hakan ne zai sa su ga cewa ana yi da su.

Hasashe dai sun nuna zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai yi mulki na hadin kai don haka akwai yiwuwar mika kujerar shugaban majalisar dattawa yankin kudu ta gabas don daidaito.

Shugaban kasa dai dan kasar Yarbawa ne yayin da mataimakinsa ya fito daga arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel