Zaben Gwamna: Jam'iyyar APC Ta Bukaci Jama'a Da Su Guji Zabar Wasu Yan Takara a Jihar Ogun

Zaben Gwamna: Jam'iyyar APC Ta Bukaci Jama'a Da Su Guji Zabar Wasu Yan Takara a Jihar Ogun

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Ogun ta yi wani jan hankali ga mazauna jihar gabannin zaben gwamnoni
  • APC mai mulki ta ce akwai wasu yan takara da suka tara dukiyar haram suke kokarin siye kuri'un mutane da kudin haram
  • A ranar Asabar, 18 ga watan Maris ne za a gudanar da zaben gwamnoni a fadin jihohi 28

Ogun - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi kira ga mazauna jihar Ogun da kada su zabi yan takarar gwamna da ke da ayar tambaya a kan tushen arzikinsu a zaben ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Jam'iyyar ta kuma bukaci masu zabe da su fito kwansu da kwarkwatansu sannan su zabi dan takararta kuma gwamna mai ci, Dapo Abiodun, rahoton Daily Trust.

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun
Zaben Gwamna: Jam'iyyar APC Ta Bukaci Jama'a Da Su Guji Zabar Wasu Yan Takara a Jihar Ogun Hoto: @dabiodunMFR
Asali: Twitter

APC wacce ta yi kiran a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris ta bayyana cewa gwamnan ya yi namijin kokari kuma ya cancanci a sake zabarsa a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Da walakin: Tinubu zai gana da zababbun 'yan majalisu da sanatoci kan wata bukata daya

Sakataren labarai na jam'iyyar, Tunde Oladunjoye wanda ya bayyana hakan a garin Abeokuta, babban birnin jihar, ya koka cewa irin wadannan yan takara na shirin siye kuri'u da kudin haram.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ya kamata mutanen jihar Ogun su cika aiki a zaben gwamna da majalisar dokoki kasancewar sun zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin zabbaben shugaban kasa.

Yace hanya daya da za su bi don cin ribar wahalar da suka yi da kuma amfana daga shugabancin Bola Tinubu shine zabar Prince Dapo Abiodun da yan takarar APC a zabe Asabar mai zuwa.

Ku lura da wadanda za su yi amfani da kazamin dukiya wajen siye kuri'unku, APC

Sai dai kuma, ya gargadi masu zabe da su zamo masu lura da mutanen da suka tara dukiya ta hanyar haram da kokarin siye mutane da kudi, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

2023: CAN Ta Fada Wa Kiristoci Yan Takarar Da Za Su Kada Wa Kuri'a A Zaben Gwamnoni Da Majalisar Jiha

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

"Ya zama dole jam'iyyar ta fito fili ta fada, saboda kore shakku, cewa jiharmu ta Ogun ba ta siyarwa bace. Duk koma ta wacce hanya suka samu lalatacciyar dukiyarsu ko nawa za su bayar, jihar Ogun ba ta siyarwa bace.
"Jihar Ogun ta samu gagarumin ci gaba a bangaren tattalin arziki kuma an samu gagarumin ci gaba da ba a taba gani ba a shekaru uku da watanni tara da suka gabata da ba za mu iya yarda mu yi wasa da makomar kasarmu mai albarka ba."

Jam'iyyun siyasa 10 sun yi maja da PDP a Ogun

A wani labarin kuma, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa wasu jam'iyyun siyasa 10 da wasu mambobin jam'iyyar APC da suka fusata sun hade da ita a jihar Ogun gabannin zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel