Gwamnan CBN Ya Shiryawa Tinubu Sababbin Makarkashiya a Zaben Gwamnoni
- Ana zargin Gwamnan babban banki ya shirya yadda Jam’iyyar LP za ta lashe zaben Gwamnan Legas
- Godwin Emefiele ya bada sababbin N500m da nufin Gbadebo Rhodes-Vivour ya yi nasara wajen neman takara
- Rhodes-Vivour yana kokarin hana Babajide Sanwo-Olu yin tazarce, zai kifar da daular Bola Tinubu a Legas
Abuja - Ana zargin Godwin Emefiele yana amfani da kujerarsa ta Gwamnan babban bankin kasa, wajen kutsawa cikin harkar siyasa a Najeriya.
Wani rahoto da The Nation ta saki a ranar Litinin, ya bayyana cewa Gwamnan bankin na CBN yana kokarin kawowa APC cikas a zaben Jihohi.
Zargin da ake yi shi ne Godwin Emefiele wanda ya ki yin biyayya ga hukuncin kotun koli a kan canjin kudi, yana yakar Jam’iyya mai-mulki a Legas.
Idan labarin ya tabbata, babban bankin na Najeriya ya ba jam’iyyar LP ta reshen jihar Legas Naira Miliyan 500 na sababbin kudi da aka fito da su a bana.
LP ta samu rabin Biliyan
Rahoton ya ce an fahimci bankin CBN ya ba ‘Yan LP rabin Biliyan a matsayin gudumuwar Gwamnan babban bankin da nufin a karbe jihar Legas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiya ta ce amfanin hakan shi ne Gbadebo Rhodes-Vivour ya samu kudin kashewa a zabe domin ya doke Babajide Sanwo-Olu da Olajide Adediran.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu yana neman tazarce a karkashin APC, sai Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor yana takara a jam’iyyar PDP.
Ana amfani da sojojin kasa
Bayan haka, jaridar ta ce Mista Emefiele ya hada kai da wani babban sojan kasa da za ayi amfani da shi domin ganin jam’iyyar ta LP tayi murdiya a Legas.
Wuraren da ake so jami’an tsaro su taimakawa Gbadebo Rhodes-Vivour wajen gwabje APC sun hada da Ajah, Lekki, Amuwo-Odofin, Ojo, Alaba da kuma Iba.
Akwai zargin sojoji sun je fadar Mai martaba Elegushi na kasar Ikate, su ka ci zarafin magoya bayan APC, arki Saheed Elegushi yana goyon bayan Tinubu.
Zaben Shugaban kasa
A zaben Gwamna, jam’iyyar APC ta na fuskantar kalubale daga jam’iyyar adawa ta LP a Legas ganin an ji Peter Obi ya doke Bola Tinubu a babban zabe.
Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu mutumin Legas ne, tun 1999 ake ganin cewa shi yake juya akalar siyasar jiha mafi arziki a Najeriya.
Asali: Legit.ng