Muhimman Abubuwan Sani Game Da Ƴan Takarar Gwamnan Borno 2

Muhimman Abubuwan Sani Game Da Ƴan Takarar Gwamnan Borno 2

A ranar Asabar, 18 ga watan Maris ne dai za a fafata zaɓen gwamnoni a faɗin tarayyar Najeriya.

Ƴan Najeriya da dama za su yi dafifi su fito a wannan ranar domin zaɓar ƴan takarar da suka kwanta musu a rai.

Legit Hausa tayi duba kan wasu muhimman abubuwa da ya kamata al'umma su sani dangane da manyan ƴan takarar gwamnan jihar Borno.

A jihar Borno takarar neman kujerar gwamnan jihar tafi zafi ne a tsakanin gwamna mai ci a yanzu Babagana Umara Zulum, na jam'iyyar APC da Mohammed Aliyu Jajari na jam'iyyar adawa ta PDP.

Babagana Umara Zulum na jam'iyyar APC

1. Haihuwa

An haifi Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar 25 ga watan Agustan 1969, a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zulum
Farfesa Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Borno Hoto: Vanguard
Asali: UGC

2. Karatu

Yayi karatun firamaren sa a Mafa daga 1975 zuwa 1980. Ya kammala karatun sakandiren sa a Monguno a shekarar 1985. Rahoton NewsWire NGR

Ya samu shaidar kammala karatun Difloma daga Ramat Polytechnic a fannin Injiniyan ruwa a shekarar 1988. Daga 1990 zuwa 1994 ya samu shaidar karatun injiniyan aikin gona a jami'ar Maiduguri.

3. Aiki

Ya fara aiki a shekarar 1989 a ma'aikatar noma ta jihar a matsayin mataimakin jami'in fasaha. A shekarar 1990 ya koma babban mai kula da filayen jiragen sama a ma'aikatar haɗin kan ƙananan hukumomi ta jihar.

A shekarar 2000 ya fara aiki da jami'ar Maiduguri a matsayin mataimakin lakcara inda ya kai har matsayin farfesa.

4. Siyasa

Farfesa Zulum ya fara siyasa ne a shekarar 2015 lokacin da aka naɗa shi kwamishinan sake gine-gine, gyare-gyare da sake matsugunnai. Muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 2018.

A shekarar 2019 yayi takarar gwamnan jihar Borno inda ya samu nasara.

5. Iyali

Farfesa Babagana Umara Zulum yana auren Dr Falmata Umara Zulum, kuma auren su Allah ya albarka ce shi da ƴaƴa masu yawa.

Mohammed Ali Jajari na jam'iyyar PDP

1. Haihuwa

An haifi Mohammed Ali Jajari a shekarar 1980 a ƙaramar hukumar Mobbar ta jihar Borno

Jajari
Mohammed Ali Jajari, Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Borno Hoto: Premium Times
Asali: UGC

2. Karatu

Mohammed Ali Jajari yayi karatun firamare da sakandire. Daga nan ya zarce zuwa jami'a. Yanzu yana da matsayin kwalin digirin digir.

3. Aiki

Ɗan takarar gwamnan Borno na jam'iyyar PDP, hamshaƙin ɗan kasuwa ne. Rahoton Kimareporters

4. Siyasa

Jajari ya fito takarar gwamnan jihar Borno a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP. Ya samu nasara a zaɓen fidda gwanin da ƙuri'u 487.

Yana fatan karɓe mulkin jihar Borno a zaɓen gwamnan da za a yi.

Muhimman Abubuwa 10 Game Da Nasiru Yusuf Gawuna Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

A wani labarin na daban kuma, an yi duba kan wasu muhimman abubuwa guda goma game da rayuwar ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar APC.

Nasiru Yusuf Gawuna shine zai nemi zama magajin Ganduje a zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel