Bankuna Ba Zasu Rufe Harkokin Hada-Hadar Kuɗi Ba Saboda Zabe

Bankuna Ba Zasu Rufe Harkokin Hada-Hadar Kuɗi Ba Saboda Zabe

  • Kungiyar Manajojin bankunan ƙasuwanci a Najeriya ta musanta labarin da ke yawo a soshiyal midiya kan zabe
  • Labarin ya yi ikirarin cewa CBN zai dakatar da hada-hadar bankuna da tura kudi ta Intanet na tsawon kwanaki 5
  • A cewar ACAMB, labarin ƙarya ne tsagwaro kuma babu kamshin gaskiya, komai zai tafi kamar yadda aka saba

Ƙungiyar shugabannin bankuna ta ƙasa (ACAMB) ta bayyana cewa dukkan rassan bankuna da hanyoyin hada-hadar kuɗi da intanet zasu ci gaba da aiki kamar yadda aka saba kafin, ranar da kuma bayan zaɓe.

ACAMB ta faɗi haka ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na kasa, Mista Rasheed Bolarinwa, ranar Laraba a Legas, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Bankuna a Najeriya.
Bankuna Ba Zasu Rufe Harkokin Hada-Hadar Kuɗi Ba Saboda Zabe Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A cewar kungiyar babu wani umarni kai tsaye daga CBN zuwa bankunan ajiya wansa ya nemi su rufe harkokin hada-hadar kudade tsawon kwanaki biyar kamar yadda labarin ƙaryan da ake yaɗawa ya yi ikirari.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Dalilan da Suka Sa EFCC Ba Ta Damke Ko Mutum Ɗaya Ba Kan Karancin Naira

"An ja hankalinmu kan wani labari da ke yawo a soshiyal midiya cewa CBN ya shirya dakatar da hada-hadar bankuna na kwana 5 daga 23 zuwa 27 ga watan Fabrairu, 2023 saboda zaɓen ranar Asabar."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"ACAMB ta tabbatar da cewa wannan labari karya ce baki ɗayansa kuma muna kara tabbatarwa yan Najeriya da Kwastomomin bankuna cewa ko kaɗan babu ƙanshin gaskiya a labarin."
"Har zuwa yau babu wani banki ko wata ma'aikatar da take gudanar da harkokin kuɗi da ta samu umarni kai tsaye daga CBN cewa a rufe bankuna ko hanyoyin tura kuɗi ta Intanet saboda zaɓe."

Bugu da ƙari, ACAMB ta bayyana cewa bankuna sun kammala duk wnai shiri na biyan bukatun kwatomominsu masu ajiyar kuɗi nan take idan sun buƙata.

Haka zalika ta yi bayanin cewa duk kwanstoman da ya yi niyyar tura kuɗi ko amfani da wata kafar da aka ware ta hada-hadar kudi ta Intanet, ba zai samu matsala ba kafin, lokacin da kuma bayan zaɓe.

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Sauran Yan Takara a Taron Abuja

Sanarwan ta ƙara da cewa babu wani abun ɗaga hankali, inda ta roki mutane su yi watsi da labarin kanzon kurege wanda wasu suka ƙirƙira da nufin haifar da ruɗani, Pulse ta rahoto.

Abinda Yasa Har Yanzu Bamu Kama Kowa Kan Karancin Naira Ba, EFCC

A wani labarin kuma Shugaban EFCC ya bayyana muhimman dalilan da suka ja hukumar ba ta damƙe kowa ba game da karancin naira

An yi tsammanin bayan bullo da tsarin sauya fasalin naira, EFCC zata sa ido kan ɓarayin da zasu maida tsoffin kuɗi bankuna ta kama su.

Sai dai Abdulrasheed Bawa, ya ce ba haka abun yake ba amma suna da shiri a ƙasa na gano waɗannan baragurbin mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel