Kamar Kananan Yara: Minista da Tsohon Shugaban Majalisa Sun Kaure da Cacar Baki

Kamar Kananan Yara: Minista da Tsohon Shugaban Majalisa Sun Kaure da Cacar Baki

  • Rt. Hon. Yakubu Dogara ya samu kan shi yana cacar baki da Ministan kwadago, Festus Keyamo SAN
  • Festus Keyamo ya maidawa Yakubu Dogara martani da ya yi kokarin taba Bola Tinubu a shafin Twitter
  • ‘Dan majalisar ya fadawa Keyamo yana gaba da shi a siyasa, Ministan ya ce ya yi masa zarra a aikinsu

Abuja - Mai magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu, Festus Keyamo da Rt. Hon. Yakubu Dogara sun yi takaddama.

Legit.ng Hausa ta bibiyi yadda ‘yan siyasan suka rika jefawa junansu maganganu a dandalin Twitter a dalilin takarar Asiwaju Bola Tinubu a 2023.

Rt. Hon. Yakubu Dogara ya rike shugaban majalisar wakilan tarayya ya soki goyon bayan da Mai girma Muhammadu Buhari yake ba ‘dan takaran APC.

Shi kuma ganin an taba Bola Tinubu, sai karamin Ministan kwadago na tarayya, Festus Keyamo ya maidawa Dogara martani, ya ce haushi yake ji.

Kara karanta wannan

Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

Festus Keyamo ya kira ‘dan majalisar Dass/Bagoro/Tafawa Balewa da cewa maci amana ne kuma karuwan siyasa, wannan bai yi wa Dogara dadi ba.

The Cable ta ce duk an yi wannan ne a shafin Twitter a ranar Lahadi, 5 ga watan Fubrairu 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon Shugaban Majalisa
Festus Keyamo da Hon. Yakubu Dogara Hoto; www.herald.ng
Asali: UGC

Martanin Keyamo ga Dogara a Twitter

“’Dan'uwana kuma abokin karatu a makarantar koyon aikin shari’a, ba ka dace da yin wannan magana ba. Ka na jin haushin goyon bayan Tinubu da Buhari yake yi ne.
Shugabannin nan biyu (yana nufin Tinubu da shugaba Buhari) sun rike abin da suka yi imani da shi, akasin kai da ka saba yawo da gantali a siyasa, ka na ci amana.

Festus Keyamo, SAN (@fkeyamo)

A siyasa, ni ba sa'anka ba ne - Dogara

A nan ne shi kuma Dogara ya fadawa Festus Keyamo, duk da sun yi karatun ilmin shari’a tare, idan aka zo harkar siyasa, ya sha gaban Ministan tarayyar.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar ya kalubalanci Keyamo da ya fara shiga takara, ya iya lashe ko da kujerar Kansila ce kafin ya tunkare shi.

A nan ne shi Keyamo wanda bai taba nasara a takara ba, ya fadawa jigon jam’iyyar PDP cewa ba da shiga zabe ne kurum ake auna nauyin ‘dan siyasa ba.

"Bari in tuna maka na kai makura a wajen aikinmu, dole ka rika girmama wanda yake gaba da kai."

— Festus Keyamo, SAN (@fkeyamo)

Atiku zai yi garambawul

Rahoto ya zo cewa ‘Dan takaran kujerar shugaban kasar na 2023 a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana manufarsa na yi wa tsarin kasa kwaskwarima.

Atiku Abubakar ya ce an kammala aiki a kan dokar yi wa kasa garambawul, ya ce a cikin watanni shida na farko za a ga canji idan ya fito da dokar a kan mulki.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Kuma Sukar Mulkin Shugaba Buhari a Gaban Jama’a Wajen Yawon Kamfe

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng