Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

  • Alamu na kara bayyana cewa takarar Bola Ahmed Tinubu ba ta samun cikakkiyar goyon baya
  • Akwai masu zargin ana yakar ‘Dan takaran na jam’iyyar APC daga cikin fadar Shugaban kasa
  • ‘Dan takaran da kan shi ya fito ya ce wahalar man fetur da canjin kudi yunkurin yakar shi ne

Abuja - A zahiri yake cewa abubuwa ba su tafiya daidai a yakin neman zaben jam’iyyar APC da ta tsaida Bola Ahmed Tinubu a matsayin ‘dan takara.

Bola Ahmed Tinubu da kan shi ya yi magana da ya je kamfe a garin Abeokuta, ya kyankyasa cewa akwai masu kokarin yi masa zagon-kasa a gwamnati.

Ana haka kuma sai aka ji Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yana jaddada wannan magana na cewa ana yakar Bola Tinubu a cikin gida.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

A rahoton da Daily Trust ta fitar, ba ta iya fadin wadanda suke kokarin hana Tinubu kai labari ba, amma zargin hakan ya yi karfi cikin ‘yan kwanakin nan.

Jawabin Gwamna El-Rufai

Malam Nasir El-Rufai ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa akwai wasu a fadar shugaban kasa da tun farko ba su so Tinubu ya samu tikitin APC ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC, tsohon Gwamnan na Legas ya gamu da adawa daga wajen Rotimi Amaechi, Yemi Osinbajo da isu Ahmad Lawan.

Taron APC
Taron yakin zaben APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Ana haka kuma sai uwargidar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta fito shafinta, tana nuna goyon baya ga abin da Gwamnan Kaduna yake fada.

Dele Alake wanda shi ne Darektan dabarun sadarwaa na kwamitin yakin neman zaben APC ya shaidawa Daily Trust cewa Bola Tinubu zai lashe zabe.

Kara karanta wannan

Muna Magana da Su – Atiku Ya Kyankyasa Yiwuwar Haduwa da Kwankwaso ko Obi

Alake ya jaddada Mai girma Muhammadu Buhari yana goyon bayan takarar Tinubu. Sai dai wasu na ganin akwai kulalliyar da ake yi a fadar shugaban kasa.

Shugaban kungiyar CODER mai kokarin gyara harkar zabe, Dr. Wunmi Bewaji ya ce alamu sun nuna akwai aikin na hannun daman Muhammadu Buhari.

Bewaji yake cewa kalaman El-Rufai sun nuna akwai masu rike da madafan iko da ba su goyon bayan Tinubu ya dare kan karagar mulki a watan Mayu nan.

Muhammad Sani Sha’aban ya bar APC

Labari ya zo cewa surukin shugaban Najeriya, Muhammad Sani Sha’aban ya bude neman takarar Gwamnan Kaduna a inuwar Action Democratic Party.

‘Dan siyasar da aka kafa All Progressives Congress da shi a jihar Kaduna ya bar Jam’iyyar, ya ce za a ga karshen talauci da rashin tsaro idan ya hau mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel