Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

  • Nasir El-Rufai ya yi karin haske a kan mutanen da ya ce su na yakar Bola Tinubu a zaben Shugaban kasa
  • Gwamnan mai shekaru 62 ya yi kaca-kaca da wadannan mutane da ake yi wa kallon Dattawan Arewa
  • El-Rufai yake cewa masu yi masu zagon-kasar ba ‘yan jam’iyya ba ne, amma su na cin alfarmar APC

Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi barazanar tona asirin wasu daga cikin mutanen da ke cin dunduniyar Asiwaju Bola Tinubu a APC.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Malam Nasir El-Rufai ya yi karin bayani a kan wadanda yace su na yakar takarar Bola Tinubu cikin fadar Aso Rock.

Gwamnan na Kaduna bai kama suna ba, amma ya tabbatar da cewa babu hannun mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo kamar yadda ake yadawa.

Kara karanta wannan

Da Gaske Buhari Ya So Ahmad Lawan Ya Maye Gurbinsa? El-Rufai Ya Warware Abun da Buhari Ya Fada Masu

Malam El-Rufai ya nuna cewa wasu dattawan Arewa ne suke kokarin goyon bayan Bola Tinubu, a cewarsa kuma su na nan a fadar Shugaban Najeriya.

Lokaci ake jira, a tona asiri

Idan lokaci ya yi, Mai girma El-Rufai ya ce zai fallasa wadannan mutane domin kowa ya san su, ya sha alwashin ganin Arewa ta marawa Tinubu baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da gwamnan ya ki yin jirwaye mai kamar wanka, amma ya nuna wadanda yake magana a kan su ba ‘yan jam’iyya ba ne, kuma ba su rike da mukamai.

Gwamna Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai da Bola Tinubu Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Legit.ng Hausa da ta saurari hirar, ta ji El-Rufai yana cewa tun ba yau ba wadannan mutane suke yakar APC duk da su na cin albarkacin jam’iyyar ne.

Daily Nigerian ta rahoto tsohon Ministan yana cewa sun yaki wadannan mutane a lokacin da suka karbe shugabancin jam’iyyar APC daga hannunsu.

Kara karanta wannan

Na Rantse Ba Wanda Muke Tsoro A Kasar Nan, El-Rufa'i Ya Mayarwa Fulogan Buhari Martani

Gwamnan ya kara da cewa a lokacin da aka fito da wani wanda su (dattawan) suke so ya zama ‘dan takaran shugaban kasa, Gwamnoni sun ci su da yaki.

Gwamnan bai iya kama suna ba a yanzu, amma ya fadawa ‘dan jaridar cewa idan ya je fadar shugaban kasa zai gan su, ya kuma ce bai jin tsoron kowa.

Ba kowane tsoho ne dattijo ba

Kamar yadda Gwamnan ya fada, akwai bambanci tsakanin dattijo irin Muhammadu Buhari da tsofaffin banza, ya ce bai ganin wani darajar tsohon kawai.

A shekara 62, Malam El-Rufai ya ce shi da takwarorinsa gwamnoni su ne asalin dattawan Arewa ba wasu wadanda ba su taba lashe zabe a Najeriya ba.

Makarkashiyar da ake yi mana - El-Rufai

A hirar da ka yi da shi, an ji Gwamnan ya na cewa ana amfani da babban bankin kasa na CBN domin ayi wa jam’iyyar APC mai mulki zagon kasa a zabe.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Daga baya an ji labari Gwamnatin tarayya ta maida martani, ta musanya zargin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel