Idan Ya Ci Zabe, Atiku Ya Bayyana Abin da Zai Yi Kafin Ya Zarce Watanni 6 a Kan Mulki

Idan Ya Ci Zabe, Atiku Ya Bayyana Abin da Zai Yi Kafin Ya Zarce Watanni 6 a Kan Mulki

  • Atiku Abubakar ya kammala shirye-shiryen yin garambawul ga fasali da tsarin da Najeriya take tafiya
  • ‘Dan takaran na jam’iyyar PDP ya yi alkawarin kawo sauyi a cikin watanni shidansa na farko a ofis
  • Okwesilieze Nwodo ya ce ‘Dan takaransu zai kawo dokar da za ta canza yadda ake gudanar da kasa

Abuja - Muddin aka zabe shi a watan nan, kuma ya zama shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce zai canza fasali da tsarin da kasar nan ta ke gudana.

Rahoton Daily Trust ta ce ‘dan takaran na jam’iyyar hamayya ta PDP ya yi wannan bayani a wajen yawon kamfe da ya je a babban birnin tarayya na Abuja.

Atiku ya zanta da masu taya shi kamfe wajen samun kuri’un ‘Yan Najeriya da ke ketare.

Dr. Okwesilieze Nwodo wanda ya wakilci Alhaji Atiku Abubakar a wajen wannan zama, ya ce sun gama nazari kan yadda za a canza fasali da tsarin kasa.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Bayanin Dr. Okwesilieze Nwodo

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Okwesilieze Nwodo shi ne mataimakin Darektan kwamitin bincike da tsare-tsaren kwamitin yakin zaben PCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewa Nwodo, abubuwa za su fi kyau ian har kowane yanki yake kula da arzikin da yake da shi.

Atiku
Atiku da mutanensa a Sokoto Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

‘Dan takaran kujerar shugaban kasar ya nuna cewa an fi samun cigaba ta fuskar walwala da tattalin arziki a lokacin da shiyyoyi ke da iko da arzikinsu.

“Idan mu na maganar doka mai cikakken iko ta farko a kan yi wa kasa garambawul, a watanni shidan farko, kasar nan za ta canza daga yadda ta ke.
An kammala wannan aiki, kuma ina jiran kurum a rantsar da ni ne a ranar 29 ga watan Mayu (2023) domin in fito da tsare-tsarena.” – Atiku Abubakar.

PDP za ta ceto Najeriya

Punch ta rahoto tsohon mataimakin shugaban kasar yana cewa abin da ake bukata a kasar nan shi ne shugabanci na kwarai, ya yi alkawarin samar da shi.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Fadawa Manoma Katon Kuskuren da Za Ayi Idan Aka Zabi Atiku

Idan ya dare mulki, ‘dan takaran babban jam’iyyar hamayyar ya ce zai ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki domin a daina yi wa kasar wani kallon banza.

2023 tsakanin Atiku da Tinubu ne

An samu rahoto cewa Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya cire irinsu Rabiu Kwankwaso da Peter Obi a lissafin zaben shugaban kasa da za ayi a bana,

Gwamnan ya ce iyakarta Obi ya samu 1% ne a Sokoto, 2% a Katsina, sai kuma 5% a Kano. A irin haka, kuri'un jihohin kudu kurum ba za su ba shi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel