Katon Kuskure ne Zaben Atiku Abubakar Inji Tsohon Hadiminsa da Ya Tona Masa Asiri

Katon Kuskure ne Zaben Atiku Abubakar Inji Tsohon Hadiminsa da Ya Tona Masa Asiri

  • Michael Achimugu ya ce ya fito da sirrin wayarsa da Atiku Abubakar ne saboda ganin zabe ya karaso
  • Tsohon hadimin ‘dan takaran ya ce akwai bukatar ya ankarar da ‘Yan Najeriya a kan zaben Atiku a 2023
  • Achimugu ya yi bayanin alakarsa da ‘dan takaran da kuma wasu sirrin da Duniya ba ta san da su ba

Abuja - Michael Achimugu ya bayyana cewa ya fallasa zargin rashin gaskiyar da Atiku Abubakar yake tafkawa ne saboda ya fadakar da al’umma.

A wata hira da aka yi da shi, Punch ta rahoto Michael Achimugu yana cewa ya dauki wayarsa da ‘dan takaran, ya watsa ne domin ya tona masa asiri.

Achimugu wanda ya yi aiki da Atiku Abubakar da yake neman takara a jam’iyyar PDP a 2019 ya ce yana so ya hana mutane yin kuskuren zabensa.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

Wannan mutum ya fadawa TVC dalilai biyu suka jawo ya fitar da sirrin wayarsa da Atiku, na farko shi ne saboda a daina raina hadiman ‘yan siyasa.

Na biyu kuma shi ne ganin zabe ya karaso, ana bukatar ilmantar da ‘Yan Najeriya domin su kauracewa yin babban kuskure wajen zaben ‘dan takaran.

Atiku Abubakar
Ayu, Atiku da Okowa Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin 'tona' asirin Atiku

"Abubuwa biyu suka jawo nayi wannan kamar yadda nayi ta nanatawa a dandalin sada zumunta.
Na farko shi ne saboda a daina raina matasa ire-irena da suka yi wa ‘yan siyasa aiki. Na biyu, in gargadi ‘yan Najeriya kafin zabe a kan yin babban kuskurensu.
Idan mutanen Najeriya su na tunanin sun ga yadda ake tafka rashin gaskiya, su jira sai sun yi kuskuren zaben Atiku Abubakar a kujerar shugaban kasa."

Kamar yaro da mahaifinsa

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

Achimugu ya shaidawa gidan talabijin cewa alakarsa da Atiku Abubakar ta zama tamkar ta ‘da da ubansa, ya ce ba zai iya fadan wasu sirrin a fili ba.

A zaman da ya yi da ‘dan takaran shugaban kasa, Achimugu ya ce ya kan tashi zuwa Dubai ya same shi domin su tattauna, ya yi masa hidima iri-iri.

Dalilin da ya sa ya ajiye sautin murya a waya shi ne saboda ya iya cika umarnin da aka ba shi domin ba kasafai ake iya yin magana da Atiku ta salula ba.

Fetur zai dawo N100

A rahoton da aka fitar a ranar Alhamis dinnan, an ji cewa a cikin watanni shida na farko a mulkin ZLP, za a saye fetur a kan N100 a gidajen man kasar nan.

‘Dan takaran jam’iyyar ZLP, Dan Nwanyanwu ya ce idan aka zabe shi, zai gyara matatun mai a cikin watanni uku zuwa hudu, kuma ya gina sababbi.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya saki layin Tinubu? Gaskiya ta fito daga bakinsa, ya bayyana komai

Asali: Legit.ng

Online view pixel