‘Dan Takara Ya Yi Alkawarin Dawo da Fetur N100 Cikin Wata 6 Idan Ya Lashe Zabe

‘Dan Takara Ya Yi Alkawarin Dawo da Fetur N100 Cikin Wata 6 Idan Ya Lashe Zabe

  • Idan Dan Nwanyanwu ya yi nasarar zama Shugaban Najeriya, farashin man fetur zai ragu sosai
  • Dan Nwanyanwu ya daukan ma kansa alkawarin ganin litar fetur bai wuce N100 a kasar nan ba
  • ‘Dan siyasar ya dauki alkawarin gina matatu tare da kawo gyare-gyare a watanni shidan farko

Abuja - Dan Nwanyanwu mai neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar hamayya ta ZLP, Dan Nwanyanwu, ya yi alkawarin rage farashin man fetur.

Dan Nwanyanwu ya dauki wannan alkawari ne yayin da aka yi hira da shi a gidan talabijin Channels a ranar Talata, 25 ga watan Junairun 2023.

Nwanyanwu yake cewa cikin watanni shida na farko da zai yi ofis, fetur zai dawo N100. A halin yanzu ana saida litar fetur akalla N220 a Najeriya.

‘Dan takaran yake cewa ya yi lissafin yadda zai cika alkawarin da ya daukarwa kansa.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan PDP ya rasu, wa zai maye gurbinsa? Ga abin da doka ta tanada

Tsarin biyan tallafin man fetur

Da aka tattauna a shirin siyasa na gidan talabijin, ‘dan takaran kujerar shugaban kasa ya yi bayanin yadda zai bullowa lamarin biyan tallafin fetur.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar ‘dan siyasar, abin kunya ne a fita da danyen mai daga Najeriya, amma sai a dawo mata da fetur, kananzir da man dizil daga kasashen waje.

Gidan mai
Gidan mai a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Vanguard ta rahoto Nwanyanwu yana bayanin yadda zai sha bam-bam da Muhammadu Buhari, ba zai nada kan shi ya zama Ministan fetur ba.

Idan har Ministan harkokin man fetur bai yi kokari ba, Nwanyanwu ya ce zai tsige shi ne domin ya kawo wanda zai yi masa irin ayyukan da yake so.

“A cikin watanni shida, za a saye fetur a kan N100 a kasar nan. Nayi lissafi, za a gyara wadannan matatun mai a cikin watanni uku zuwa watanni hudu.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Sannan za mu kafa kananan matatun danyen mai a kowane bangare. Mu na da dukiyar da za a yi wadannan abubuwa, ba a ga dama ba ne kawai.
Idan mutane su na cin moriyar wani tsari, ba za su bari a kawo gyara ba, amma ni zan yi hakan.

- Dan Nwanyanwu

Remi Tinubu za ta hau mulki

An ji labari Naja’atu Muhammad ta ankarar da 'Yan Najeriya a kan kuskuren zaben APC da Bola Tinubu a 2023, ta ce a karshe ba shi ne zai yi mulkin ba.

Naja’atu Muhammad take cewa idan jam’iyyar APC ta kafa gwamnati, matar Tinubu ce za ta rika shugabancin, ita za ta jagoranci kasar tare da wasu tsiraru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel