Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

  • Bola Tinubu ya yi kaca-kaca da Naja’atu Mohammed bayan ajiye kujerarta, ta koma wajen Atiku Abubakar
  • Raddin Bola Tinubu ya fito ne ta bakin Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC
  • A jawabin da Mahmud Jega ya fitar, ya zargi ‘yar siyasar da yaudarar mutane da nuna hadamarta a fili

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya dawo ya maida martani ga kalaman da aka ji a bakin Naja’atu Mohammed.

A ranar Litinin, Vanguard ta rahoto kwamitin yana raddi ga Naja’atu Mohammed wanda ta ajiye matsayinta na Darektan yakin takarar Bola Tinubu.

Kwamitin na PCC ya ce an fatattaki Hajiya Naja’atu Mohammed daga matsayinta ne saboda rashin sanin aiki, sannan ana zarginta da cin amanar APC.

Babban mai taimakawa ‘dan takaran APC wajen yada labarai, Mahmud Jega ya fitar da jawabi yana cewa Naja’atu Mohammed ta fake ne da murabus.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

Dama korar ta ake shirin yi - Jega

A zahirin gaskiya, Mahmud Jega ya ce Naja’atu Mohammed ta fice daga kwamitin yakin neman zaben APC ne a lokacin da ake shirin korarta daga PCC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabin da aka fitar ya kara da cewa soki-burutsun da ‘yar siyasar take yi, ya nuna cewa tun farko bai kamata ta shiga harkar hidimtawa ‘Yan Najeriya ba.

Jam’iyyar APC
Taron Yakin zaben Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: UGC

Duk da ba Likita ba ce, Jega ya ce a shekaru talatin 30 da suka wuce, ba ta da aikin da ya wuce gantali a siyasa, amma ta na maganar lafiyar Bola Tinubu.

Hadimin ya ce ko kungiyar masu magungunan gargajiya sai sun fatattaki ‘yar siyasar saboda kwamacalar da tayi wajen nuna ‘dan takaran bai da lafiya.

Tinubu ya yi wa Arewa tanadi

Bugu da kari, tsohon marubucin ya soki ikirarin da ‘yar siyasar tayi na cewa Bola Tinubu ya fada mata babu wani tanadin da ya yi wa Arewa a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin APC, Aka Ba Shi Takara - Najaatu Mohammed

“Asíwájú ya gabatar da manufofin da yake da shi ga duka Najeriya, daga ciki matsalar da ta addabi Arewacin kasar ta samu kulawa ta musamman.
Sannan Asiwaju ya halarci taron Arewa a shekarar bara, inda ya yi bayanin tsare-tsaren nan.”

- Mahmud Jega

Rahoton ya ce a karshen jawabin Jega, ya yi kira ga jama’a suyi watsi da ‘yar siyasar, ya zarge ta da hadama, ya ce a maida hankali wajen nasarar Tinubu.

Gorin Abayomi Mumuni

Kun samu labari a farkon makon nan, Abayomi Mumuni ya fitar da jawabi yana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taimakawa Bola Tinubu.

Jigon na tsohuwar jam’iyyar Congress for Progressives Change (CPC) ya ce sai an yi gyara domin Tinubu ya yi wa Buhari bakin kokarinsa a 2015 da 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel