Ni Dan a Mutun APC Ne, Ina Tare da Tinubu Dari-Bisa-Dari, Yahaya Bello Ya Magantu

Ni Dan a Mutun APC Ne, Ina Tare da Tinubu Dari-Bisa-Dari, Yahaya Bello Ya Magantu

  • Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi ya musanta jita-jitan da ake yadawa game da cewa ya daina goyon bayan Tinubu
  • An yada wasu rahotanni a baya da ke nuna cewa, Yahaya Bello ya janye daga marawa dan takarar shugaban kasa na APC baya
  • APC na ci gaba da shirin fuskantar zaben 2023, jam’iyyar na da burin ci gaba da mulki bayan shugaba Buhari

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ba da tabbacin cewa, yana goyon bayan dan takarar shugaban kasarsu na APC, Bola Ahmad Tinubu.

Hakazalika, ya ce shi dan a mutun jam’iyyar ta APC ne kuma yana goyon bayan dukkan yunkurinta da shugabancinta.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi lokacin da yake watsi da wasu rahotannin da ke zargin ya bar tsagin Bola Ahmad Tinubu.

Kara karanta wannan

'Babban Abinda Atiku Abubakar Ya Rasa Wanda Ka Iya Jawo Masa Faɗuwa a Zaben 2023'

Yahaya Bello ya magantu kan matsayarsa ga Tinubu
Ni Dan a Mutun APC Ne, Ina Tare da Tinubu Dari-Bisa-Dari, Yahaya Bello Ya Magantu | Hoto: Gov Yahaya Bello
Asali: Facebook

Ku san makamar aikinku, Bello ga 'yan jarida

Ya bukaci ‘yan jarida da masu tattaro rahotanni da su san makamar aikinsu tare da kiyaye yada jita-jita mara tushe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake zantawa da kafar yada labarai ta Channels, Bello ya tunawa INEC cewa, kundin dokar zabe ya ba ta damar kamawa tare da hukunta masu ayda labaran karya game da zabe.

A cewarsa:

“Na tashi ne naga wancan labarin yana yawo. Babu dadi kuma ina kira ga hukumomin doka da dukkan masu hannu game da aikin jarida a Najeriya su tsaya a iyakar matsayinsu.”

A goge rubutun cikin sa'o'i 24

Ya ce yana da kyau hukumomi su dauki mataki kan wadannan masu yada labaran karya tare da umartarsu da su goge rubutun cikin sa’o’i 24.

Ya kuma yi barazanar daukar matakin doka matukar ba a goge rubutun da ke yawo game da nesanta shi da Tinubu ba, rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

2023: Wani Gwamnan APC Ya Janye Daga Kamfen Bola Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Idan baku manta ba, Yahaya Bello ya fito takarar shugaban kasa a APC, inda daga baya a lokacin zaben fidda gwani ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu.

Ya ce ya matukar gamsu da matsayinsa na jagoran matasa masu tallata Tinubu daga yanzu zuwa zaben 25 ga watan Fabrairun bana.

A jihar Kano kuwa, APC ta ce za ta ba Kwankwaso mamaki ta hanyar zaban Tinubu da sauran 'yan takarar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel