Abin Ya Isa Haka: Jam’iyyar NNPP Ta Zargi ‘Yan APC da Ta’adi, Ta Ja-Kunnen Gwamna

Abin Ya Isa Haka: Jam’iyyar NNPP Ta Zargi ‘Yan APC da Ta’adi, Ta Ja-Kunnen Gwamna

  • Jam’iyyar NNPP ta na zargin ‘ya ‘yan APC da ruguza fastocin ‘yan takaranta da ke neman mulki
  • Shugaban NNPP a Borno ya ce an sauke fastocin Rabiu Musa Kwankwaso da Attom Magira Tom
  • Mohammed Mustapha yake cewa ba yau aka fara yi masu haka a mulkin Babagana Zulum ba

Borno - Jam’iyyar NNPP mai hamayya a jihar Borno, tayi kira ga Gwamna Babangana Umara Zulum da ya ja-kunnen magoya bayan APC mai mulki.

Premium Times ta ce jam’iyyar NNPP ta na zargin ‘ya ‘yan APC mai-mulki da ruguza allon wasu daga cikin ‘yan takararta a zabe mai zuwa da za a shirya.

A karshen makon da ya gabaa, NNPP ta ce wakilan jam’iyyar APC sun sauke mata fastoci 16.

Wannan bayani ya zo cikin wani jawabi na musamman da shugaban NNPP na reshen jihar Borno, Mohammed Mustapha ya fitarwa 'yan jarida.

Kara karanta wannan

Atiku ya sha romo, Kwankwaso ya karye a Arewa, 'yan NNPP 170,000 sun koma PDP a wata jiha

NNPP tayi asarar fostoci 16

Alhaji Mohammed Mustapha ya zargi mabiya jam’iyyar APC da sake lalata allon ‘yan takaransu, ya ce an yi hakan ne bayan an ruguza masu alluna 16.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin yake cewa abin kunya ne yadda jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum ta dauki siyasa da gaba a Borno.

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Nasarawa Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Shugaban na NNPP ya ce ana haka ne a lokacin da ake kiran Babagana Zulum da Gwamnan jama’a, kuma masanin boko wanda yake da lambar mni.

Jawabin Shugaban NNPP na Borno

“A ranar 20 ga watan Junairu 2023 aka rusa allon ‘dan takararmu na shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da ‘dan takaran Sanata, Attom Magira Tom
An kawo mana harin nan ne makonni biyu bayan an yi irin haka ga wasu allon takararmu.
A matsayinmu na jam’iyya mai bin doka, ba mu yi ramuwar gayya ba ko mu nemi rikici ba, sai muka kira mabiyanmu su yi hakuri, su sanar da jami’ai.”

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

- Mohammed Mustapha

Kamar yadda rahoton Leadership ya bayyana, jam’iyyar ta kafa allon ne a wasu muhimman wurare a Maiduguri da wasu garuruwan jihar Borno.

Baya ga haka, Mohammed Mustapha yace an maye gurbin hotunan da ke cikin allonsu da wasu ‘yan takaran APC, yake cewa ba yau aka saba ba.

Sai an yi gyara a APC - Mumuni

Ku na da labari jagoran APC a jihar Legas, Abayomi Mumuni ya fitar da jawabi yana cewa shugaban kasa bai taimakawa takarar Bola Tinubu da kyau.

Mumuni ya ce Tinubu ya yi bakin kokari wajen ganin nasarar Muhammadu Buhari a 2015 da 2019, amma da zaben 2023 ya karaso, sai aka watsar da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel