Mambobin Jam’iyyar NNPP da Yawa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Yobe

Mambobin Jam’iyyar NNPP da Yawa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Yobe

  • Tsohon sakataren jam’iyyar NNPP a Arewa maso Gabas ya bayyana adadin wadanda suka sauya sheka a Arewacin Najeriya
  • Ya bayyana cewa, akalla mutane 170,000 ne suka bayyana komawa PDP tare dashi a daidai lokacin da zabe ke karatowa
  • Jam’iyyar PDP na ci gaba da samun karbuwa a yankin Arewa, ana ci gaba da shirin babban zaben 2023 nan da watan Fabrairu

Jihar Yobe - An ruwaito cewa, dandazon mambobin jam’iyyar NNPP ne a jihar Yobe suka sauya sheka tare da kama hanyar PDP a gabanin zaben watan Fabarairun bana.

Dr. Babayo Liman, tsohon sakataren jam’iyyar NNPP a Arewa maso Gabas ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Damaturu a ranar Talata 24 ga watan Janairu.

Idan baku manta ba, Dr. Babayo ya sanar da sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a makwannin baya, inda ya ja zuga suka bar NNPP ta su Kwankwaso, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

NNPP Ta Ruɓe, An Bayyana Wanda Ya Kamata Kwankwaso Ya Janye Wa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

NNPP ta rasa mambobinta a jihar Yobe
Mambobin Jam’iyyar NNPP da Yawa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Yobe | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Da yake magana a Damaturu, Dr. Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Muna nan ne don sanarwa jama’a da dandazon magoya bayanmu kusan 600,000 a Arewa maso Gabas game da shawarin da muka yanke.”

Ya bayyana cewa, a Yobe, ya shigo PDP ne tare da mambobi sama da 170,000, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Dalilin da yasa ake barin NNPP

Da yake bayyana dalilin da yasa jam’iyyar NNPP ke rasa mambobinta cikin kwanakin nan, Dr. Babayo ya ce:

“Jam’iyyar bata da tsari da hangen warware matsalolin Najeriya.”

Ya kuma shaida cewa, sama da watanni biyar, jam’iyyar NNPP ta gaza warware wasu matsalolin cikin gida da take fuskanta.

Ya ce:

“Saboda haka, na yanke shawarin ajiye mukami na tare da shiga PDP don marawa dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar.
“Kamar yadda aka saba, yayin da shugaba ya fice daga wata jam’iyyar siyasa zuwa wata, yana bukatar sanar da magoya bayansa shawarin da ya yanke.”

Kara karanta wannan

Kyau Kwankwaso Ya Hakura – Kungiya ta Kawo Hujjoji Kan Wanda Arewa Za Ta Zaba

“Don haka, na dauke shi a matsayin nauyi da ke kaina na zaga jihohi shida na Arewa maso Gabas don sanar da magoya bayana shawarin da na yanke da matsayata.”

PDP alheri ce ga ‘an Najeriya

A cewar Dr., shekaru 16 da PDP ta yi tana mulki sun kasance mafi dadi da nasara ga ‘yan Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa, rashin tsaro ana samunsa ne a wasu bangarori kadan na Najeriya, sabanin yadda gwamnatin APC ta jawo yaduwar barna a dukkan yankunan kasar.

A tun farko Dr. Babayo ya ce akalla mambobin NNPP miliyan 2.8 ne suka sauya sheka a yankin Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel