2023: Bola Tinubu Bai Samun Goyon Baya da Kyau - Jigon APC Ya yi wa Buhari Gori

2023: Bola Tinubu Bai Samun Goyon Baya da Kyau - Jigon APC Ya yi wa Buhari Gori

  • Abayomi Mumuni ya raina kokarin da shugaba Muhammadu Buhari yake yi wa Bola Tinubu
  • A wani jawabi da ya fitar, Abayomi Mumuni ya ce Buhari bai rama abin da Tinubu ya yi masa ba
  • ‘Dan siyasar ya bada labarin yadda ‘dan takaran APC ya taimaki shugaban kasar a 2015 da 2019

Lagos - Abayomi Mumuni wanda ya taba yi wa jam’iyyar CPC takarar Gwamnan jihar Legas, ya zargi shugaban kasa da kin goyon bayan Bola Tinubu.

Vanguard ta rahoto Abayomi Mumuni yana mai cewa Asiwaju Bola Tinubu bai samun isasshen goyon bayan da ya dace a wajen Muhammadu Buhari.

Abayomi Mumuni yana so Buhari ya maimata irin taimakon da Bola Tinubu ya yi masa a lokacin da ya tsaya takarar shugabancin Najeriyan a zaben 2015.

Kara karanta wannan

APC Ta Ga Jama’a a Kamfe, Ta Ce Gwamnan PDP Ya Tattara Kayansa Daga Gidan Gwamnati

A ra’ayin jigon na jam’iyyar APC mai mulki a Legas, akwai bukatar shugaban Najeriyan ya kara kokarin wajen ganin ya taimakawa ‘dan takaransu.

Abayomi Mumuni ya saki jawabi

‘Dan siyasar yana cikin ‘yan sashen tsaro na kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar ta ce an fahimci hakan ne bayan tsohon ‘dan takarar Gwamnan ya fitar da jawabi ta bakin hadiminsa, Rasheed Abubakar a karshen makon jiya.

Bola Tinubu
Shugaban kasa ya ba Bola Tinubu tuta a Bauchi Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Mumuni yake cewa Tinubu, magoya bayansa da sauran ‘yan jam’iyyar APC su na bukatar shugaban kasa ya dage wajen mara masu baya a zaben bana.

Abin da Tinubu ya yi wa Buharia baya

A zabukan 2015 da 2019, Mumini yake cewa tsohon Gwamnan Legas ya goyi bayan Buhari, ya goye shi tamkar ‘dan jariri a bayan shi domin ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

Ganin halin da aka shiga yanzu, ‘dan jam’iyyar ta APC ya ce zai yi kyau shugaban kasa ya yi halacci.

A jawabin da ya fitar, ‘dan siyasar ya ce shi da Buhari sun sha kashi da suka yi takara a ANPP da CPC, ba su iya samun nasara ba sai da aka dunkule a APC.

Amma duk da korafin da Muminu yake yi, ya bayyana cewa Asiwaju zai yi nasara a zaben da za ayi, ya kuma ce ‘dan takaran ya fi cancanta ya rike Najeriya.

Wike yana tare da APC?

An ji labari shugaban karamar hukumar da Rotimi Amaechi ya fito, ya bayyana ‘dan takaransu. Samuel Nwanosike ya tabbatar da ba za su bi Atiku Abubakar ba.

Kamar yadda kalaman Hon. Samuel Nwanosike suka nuna, Gwamna Nyesom Wike ya rabu da Peter Obi da Atiku Abubakar, zai tallata Bola Tinubu a jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel