APC Ta Ga Jama’a a Kamfe, Ta Ce Gwamnan PDP Ya Tattara Kayansa Daga Gidan Gwamnati

APC Ta Ga Jama’a a Kamfe, Ta Ce Gwamnan PDP Ya Tattara Kayansa Daga Gidan Gwamnati

  • Jam’iyyar APC ta fara hango kan ta a gidan Gwamnati, ta sha alwashin karbe mulki a Bauchi
  • Yakubu Murtala-Ajaka ya fadawa Gwamna Bala Mohammed ya some rubuta takardar wasiyya
  • Mataimakin sakataren yada labaran APC ya ce Bola Tinubu da Sadique Abubakar za su ci zabe

Bauchi - Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta fadawa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed ya fara shirin barin kan karagar mulki.

A rahoton da Tribune ta fitar a ranar Litinin, an ji Yakubu Murtala-Ajaka yana cewa jam’iyyarsu ta APC za tayi waje da Gwamnatin Bala Mohammed.

Mataimakin sakataren yada labaran APC na kasa ya bayyana haka da ya samu damar jawabi a taron yakin neman zaben Bola Tinubu a Bauchi.

Yakubu Murtala-Ajaka yake cewa APC tana da duk abin da ake bukata domin lashe zabe.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

Bauchi sai Air Marshal Sadique Abubakar

An rahoto Murtala-Ajaka yana cewa su na sa ran Air Marshal Sadique Abubakar mai ritaya zai yi galaba a zaben 11 ga watan Maris, ya karbe mulkin jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin na APC ya ce tsohon sojan ya cancanci kuri’un mutanen Bauchi domin ya rike amanar Najeriya a lokacin da yake shugaban hafsun sojin sama.

Kamfen APC
Muhammadu Buhari, Bola Tinubu da Sadique Abubakar Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Kwanan PDP ya zo karshe - APC

A cewar Mataimakin sakataren yada labaran na jam’iyyar APC, dinbin mutanen da aka gani wajen taron Bola Tinubu ya nuna kwanan PDP ya zo karshe.

Daily Trust ta ce a jawabin da ya gabatar, Yakubu Murtala-Ajaka ya godewa mutanen da suka cika filin wasa domin su farantawa ‘dan takaran na APC rai.

‘Dan siyasar yake cewa Bola Tinubu mutum ne mai cika duk alkawarin da ya dauka, saboda haka ba zai manta da irin alherin mutanen garin Bauchi ba.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Bai Samun Goyon Baya da Kyau - Jigon APC Ya yi wa Buhari Gori

“(Bola Tinubu) ba zai manta da kaunar nan da ya samu yau a garin Bauchi a wajen taron yakin neman zaben shugaban kasarmu ba.”
Nan da 25 ga watan Fubrairun 2023, zai bayyana ga ‘Yan PDP a Bauchi cewa ta su ta zo karshe. PDP ta fara rubuta wasiyyar barin mulki.”

- Yakubu Murtala-Ajaka

Tazarcen Bala Mohammed

Idan za ku tuna, a can baya mun kawo jerin Gwamnonin Jihohin da sai sun yi da gaske za su koma mulki a Najeriya saboda barazanar 'yan adawa.

A cikinsu akwai Gwamna Bala Mohammed da Umaru Fintiri a Arewa maso gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel