Kujerarsu ta na rawa: Gwamnonin Jihohi 4 da Sai Sun Yi da Daske Za Su Koma Mulki

Kujerarsu ta na rawa: Gwamnonin Jihohi 4 da Sai Sun Yi da Daske Za Su Koma Mulki

  • A watan Maris mai zuwa, Hukumar INEC za ta gudanar da zaben Gwamnoni a mafi yawan Jihohi
  • Mafi yawan Gwamnonin kasar nan sun kammala wa’adinsu, don haka za a zabi sababbin Gwamnoni
  • Amma akwai wasu Jihohin da Gwamnoninsu ke neman tazarce domin su shiga wa’adinsu na karshe

Nigeria - A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta bibiyi yadda siyasa ta ke tafiya, ta kawo jerin Gwamnonin da ta ke ganin za a kai ruwa-rano wajen tazarcensu.

Akwai Gwamnoni irinsu Babagana Zulum, Bello Matawalle, Mala Buni da Babajide Sanwo Olu da mu ke ganin kalubalensu bai kai na takwarorinsu ba.

Ga jihohin da muke ganin Gwamnoni masu-ci su na da aiki a gabansu:

Jihohin da za a kai ruwa-rana:

1. Bala Mohammed

Bala Mohammed yana da kalubale a gabansa wajen komawa kan kujerar Gwamnan Bauchi domin tun daga cikin PDP akwai manyan jam’iyyar da ke yakan tazarcensa.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya samu sabani da manyan ‘yan siyasa da-dama, sannan yana fuskantar Air Marshall Siddique Abubakar mai ritaya da Sanata Halliru Jika a APC da NNPP.

2. Umaru Fintiri

Babbar kulubalen Gwamna Umaru Fintiri na jihar Adamawa ita ce Sanata Aisha Binani mai takara a APC, wanda ita kadai ce macen da ke neman Gwamna a Arewa.

Gwamnonin Jihohi
Wasu Gwamnonin Najeriya Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Tsayawa takarar Binani ta jawo Fintiri ya canza ‘dan takarar mataimakin gwamnansa, ya dauko mace domin tsoron mutane su karkata wajen zaben mace.

3. Inuwa Yahaya

Wani Gwamna a jerin na mu shi ne Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe wanda ya karbe mulki daga hannun Gwamnatin PDP a zaben 2019 a karkashin APC.

Duk da ana ganin sai PDP tayi da gaske a Gombe, Yahaya yana fuskantar barazana har daga NNPP wanda ta tsaida Hon. Khamisu Mailantarki a matsayin ‘dan takara.

Kara karanta wannan

"Gwamnoni 11 da Sanatocin Jam’iyyar APC 35 Suna Yi wa Atiku Aiki a Boye a Arewa"

4. Seyi Makinde

Akwai ‘yan sabanin cikin gida nan da can a jam’iyyar PDP na reshen jihar Oyo saboda takarar Atiku Abubakar, wannan zai iya yi wa Gwamna Seyi Makinde tasiri.

A zaben shekarar nan, da-alama sai PDP ta dage a Oyo domin jam’iyyar APC za tayi da gaske wajen ganin ta karbe iko da duka jihohin da ke Kudu maso yamma.

Bala na cikin matsala?

An ji labari cewa Muhammadu Bello Kirfi ya yi kaca-kaca da Gwamnatin Bala Mohammed, ya ce tun da aka karbe masa sarauta, Gwamnan Bauchi ba zai zarce ba.

Tsohon Wazirin na Bauchi ya ce su ne su kayi wa Bala Mohammed riga da wando domin ya zama Gwamna a 2019, amma ya juya masu baya da ya dare kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel