Jagororin Kirista Sun Fadawa Mabiyansu Wadanda Za Su ba Kuri’arsu a Zaben 2023

Jagororin Kirista Sun Fadawa Mabiyansu Wadanda Za Su ba Kuri’arsu a Zaben 2023

  • Limaman cocin katolika da ke Kudu maso yammacin Najeriya sun yi zama na musamman a Ibadan
  • Malaman addinin sun ce akwai bukatar jama’a su zabi shugaban da ba zai nunawa kowa bambanci ba
  • Ba tare da kama sunan wani ‘dan takara ko jam’iyya ba, Fastocin sun yi magana a kan batun rashin tsaro

Ekiti - Limaman cocin katolika na Kudu maso yammacin Najeriya sun yi kira ga mutane da su zabi shugabanni nagari a zabe mai zuwa.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa malaman addinin na kirista sun fadawa mabiyansu su zabi ‘yan siyasar da za su zama masu kishin al’ummarsu.

Haka zalika an bukaci mutane su kada kuri’arsu ga shugabannin da za su bauta masu, kuma su magance matsaloli ba tare da nuna bambani ba.

Fastocin su na ganin akwai bukatar kawo karshen rashin tsaro da matsin lambar rayuwa.

Kara karanta wannan

Ba Wanda Zai Ci Bulus: Atiku Ya Gindaya Sharadin Baiwa Mambobi da Manyan PDP Mukami Idan Ya Ci Zabe

Fastocin garuruwa sun taru a Ibadan

Kamar yadda bayani ya fito bayan taron, wannan zama da aka yi ya tattaro limaman katolika daga garuruwan Ilorin, Ondo, Ekiti, Oyo da Osogbo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar limaman da sakatarensa, Rabaren Gabriel Abegunrin da Rabaren John Oyejola suka sa hannu a takardar bayanin taro da aka fitar.

Kirista
Wasu limaman Kiristoci a Aso Villa Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Rabaren Felix Femi Ajakaye ya yi wa ‘yan jarida bayanin makasudin haduwarsu.

Fito da Amotekun ya taimaka - Fastoci

A wajen taron Fastocin sun yabi Gwamnonin Kudu maso yamma da suka yi kokari wajen kafa dakarun WNSN wadanda aka fi sani da Amotekun.

Malaman addinin suke cewa kirkiro Amotekun da aka yi, ya taimaka wajen rage matsalar tsaro da ya addabi mutanen da ke zama a jihohin yankin.

Punch ta ce kafin Fastocin su tashi daga taron, sai da suka yi Allah-wadai da kisan wani babban limamin katolika da ke aiki a garin Minna, Isaac Achi.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Gwamnonin Jihohi 36 Za Su Titsiye Gwamnan Babban Bankin CBN

A karshe, fastocin sun yi kira ga shugabanni su yi adalci a maganarsu da aikinsu domin ganin an shirya zabe mai inganci a watannni masu zuwa.

Bakin cikin da aka yi MKO Abiola

Ana zargin Marigayi MKO Abiola yake kan gaba a zaben da aka shirya a 12 ga watan Yunin 1993, kwatsam sai gwamnatin Babangida ta tsida zaben.

An samu labari cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo yana ganin bakin ciki ya hana MKO Abiola darewa kan karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel