Ana wata ga wata: Gwamnonin Jihohi 36 Za Su Titsiye Gwamnan Babban Bankin CBN

Ana wata ga wata: Gwamnonin Jihohi 36 Za Su Titsiye Gwamnan Babban Bankin CBN

  • Kungiyar gwamnonin Najeriya za tayi zama da Gwamnan babban banki watau CBN, Godwin Emefiele
  • Godwin Emefiele zai yi wa Gwamnonin jihohi makasudin canza Naira da yin kaidi a kan cire kudi a rana
  • Sanarwar da Kungiyar NGF ta fitar a daren yau ya tabbatar da cewa a yammacin Alhamis za ayi zaman

Abuja - Kungiyar NGF ta gwamnonin Najeriya ta gayyaci Gwamnan babban banki na kasa, Godwin Emefiele zuwa wani taro na musamman a gobe.

Jaridar Premium Times ta ce gwamnonin jihohi za su yi taron da gwamnan na CBN ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Junairu 2023 ta kafar yanar gizo.

Makasudin tattaunawar ita ce Godwin Emefiele ya yi bayanin abin da ya sa babban bankin Najeriya watau CBN ya canza wasu takardun kudin kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Babban Banki Ya Koma Bakin Aiki, CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa

Baya ga haka, Mista Emefiele zai samu damar yi wa Gwamnonin jihohin karin haske game da tsarin da aka fito da shi na takaita cire kudi a bankuna.

Sanarwa ta fito daga kungiyar NGF

Vanguard ta ce shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya bada wannan sanarwa ranar Talata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kungiyar NGF ta ce zaman nan zai bada damar ganawa tsakanin masu ruwa da tsaki daga bangaren gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Babban Bankin CBN
Gwamnan Bankin CBN a taro Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

A dalilin haka, ana sa ran za a samu mafita a kan matsalolin da ake fuskanta a kasar a sakamakon canza manyan takardun Nairori da bankin CBN ya yi.

Rahoton ya ce taron na gobe zai tattauna tasirin wannan tsari kan tattalin arzikida kuma tsaron kasa.

Za a zauna da karfe 9:00 - Asishana Okauru

Kara karanta wannan

Rudani: Ta karewa gwamnan CBN yayin da jami'an DSS ta mamaye ofishinsa da yamma

Darekta Janar na NGF, Asishana Okauru ya bayyana cewa da karfe 9:00 na dare za a fara taron. The Cable ta fitar da wannan rahoto a farkon makon nan.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma Mai girma Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal shi ne wanda ya kira wannan zama da za ayi.

Tun bayan da babban bankin da Godwin Emefiele yake jagoranta ya canza takardun kudi, ya kuma rage adadin kudin za a iya cirewa a kullum, ake ta surutai.

Fallasar Muhammad Gudaji Kazaure

An ji labari ‘Dan Majalisar tarayyar nan, Muhammad Gudaji Kazaure ya fito fili ya fadawa Duniya irin ‘barnar’ da ake tafkawa a boye a babban bankin CBN.

Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana yadda Gwamnan babban banki, Godwin Emefiele ya saye manya, ya ce a boye ake kawo kasafin kudinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel