Shekaru 30 da Rushe Zabe, Obasanjo Ya Tona Abin da Ya Hana a Mikawa Abiola Mulki

Shekaru 30 da Rushe Zabe, Obasanjo Ya Tona Abin da Ya Hana a Mikawa Abiola Mulki

  • Olusegun Obasanjo ya halarci bikin da aka shirya domin murnar cikar BBHS shekaru 100
  • Tsohon shugaban kasar Najeriyan yana cikin daliban da makarantar nan ta yaye a shekarun 1950s
  • A wajen lacca da aka yi, Obasanjo ya dauko maganar Marigayi MKO Abiola wanda ya yi karatu a BHHS

Ogun - A wata tattaunawa da aka yi da shi, tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi bayanin abin da ya hana Cif MKO Abiola mulki.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa a ranar Laraba, Cif Olusegun Obasanjo ya gabatar da wata lacca mai taken “Eyin Ni Iwe Wa” a Abekouta, jihar Ogun.

An shirya laccar ne domin bikin murnar cikar shekaru 100 da kafa makarantar Baptist Boys High School wanda shi da MKO Abiola suka halarta.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Yi Mani Alkawarin N10m Domin Yi Wa Bukola Saraki Sharri – ‘Dan Fashi

A wajen jawabin da yayi ne, Obasanjo wanda ya rike Najeriya a lokacin mulkin soja da na farar hula, yayi magana a kan tsohon ‘dan makarantar ta su.

An yi wa Abeokuta bukulun mulki

An rahoto tsohon sojan yana mai cewa bakin ciki ne kurum ya hana a kyale wani mutumin kasar Abeokuta watau Abiola, ya zama shugaban Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Makarantar nan ce ta yaye irinsu Obafemi Awolowo da sauran manyan mutane a Najeriya.

Obasanjo
Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images
"Saboda makarantar BBHS ne na zama abin da na zama a yau.
A yau akwai tsofaffin ‘yan makarantar nan a ko ina; kamfanoni, makarantu, gidan soja da sauran aikin damara, kungiyoyi masu zaman kansu da gidan sarauta.
Misali shi ne shugaban kungiyar tsofaffin daliban BHHS, Farfesa Kayode Oyesiku."

- Olusegun Obasanjo

Makarantar BHHS ta ciri tuta

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tono Asalin Matsala, Ya Fadi Abu Ɗaya Tak Da Ya Kawo Yan Bindiga Arewacin Najeirya

Vanguard ta ce Obasanjo ya bada misali da kan shi, ‘dan gidan ba kowa ba da ya shiga soja, aka yi yaki, har ya kai ga rike Najeriya a karo biyu.

"Kuma akwai MKO Abiola, wanda ya fara zama attajiri da harkar sadarwa, wanda ake tunanin ya lashe zaben 1993 na zama shugaban kasar Najeriya.
Ba don bakin ciki ba, da MKO Abiola ya zama shugaban kasa kamar ni, da an samu karin tsohon ‘dan makarantar BBHS bayan ni da ya rike mulki."

- Olusegun Obasanjo

Tinubu zai hade da SDP?

An samu rahoto cewa bisa dukkan alamu APC za ta hada-kai da Jam’iyyar adawa ta SDP domin a dankara su Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da kasa.

Wani jami’in Jam’iyyar SDP, Alfa Muhammad ya ce tun a shekarar 2020 ake tunanin haduwa da Bola Tinubu, yanzu sun samu wannan dama a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Asali: Legit.ng

Online view pixel