Ku Nuna Sakamakon Yankinku Na Baku Mukami Ko Kwangila, Atiku Ga Mambobin PDP

Ku Nuna Sakamakon Yankinku Na Baku Mukami Ko Kwangila, Atiku Ga Mambobin PDP

  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, yace ba wanda zai ci banza ya samu mukami a gwamnatinsa
  • Atiku ya bayyana sharadin da zai gindaya wa kowane mamba ko jigon PDP ƙafin naɗa shi mukami ko ba shi wata kwangila
  • Tsohon mataimakin shugaban kasan ya fadi haka ne a zauran ganawa da masu ruwa da tsaki a Abeokuta, babban birnin Ogun

Ogun - Ɗan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya faɗa wa mambobim jam'iyyarsa PDP sharadin da zai sa kafin ya basu muƙami ko kwangila idan Allah ya ba shi mulki a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace ya zama wajibi mambobin PDP su gabatar da sakamakon rumfar zabensu matukar suna son amfana da gwamnati.

Atiku a Ogun.
Ku Nuna Sakamakon Yankinku Na Baku Mukami Ko Kwangila, Atiku Ga Mambobin PDP Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Atiku ya jaddada cewa idan kowane mamba da jiga-jigan PDP zasu kawo rumfunan zaɓensu, to cikin ruwan sanyi jam'iyyar zata samu nasara a zaben.

Kara karanta wannan

Wike Ya Samu Tangarɗa, Gwamnan G-5 Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Yuwuwar Haɗewa da Atiku

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku ya faɗi haka ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun yayin ganawa da masu ruwa da tsaki ranar Laraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baya ga masu ruwa da tsaki da magoya bayan PDP, kusan kungiyoyi 72 ne suka halarci wurin taron yau Laraba 18 ga watan Janairu, 2023.

Da yake amsa tambayoyin mahalarta taron, Atiku yace:

"Dukkanku mambobi da magoya bayan PDP. Idan kuna son PDP ta koma kan mulki ina rokonku dan Allah ku tabbata mun samu galaba a rumfar zabenku."
"Batun kuna bin dan takarar majalisar tarayya, gwamna, Sanata ko dan takarar shugaban kasa zuwa wuraren kamfe bai isa ya sa ku samu mukami ba, ba zai sa ku sami Kwangila a matakin karamar hukuma, jiha ko tarayya ba."
"Hanya ɗaya ce a wurina idan har na zama shugaban kasa, idan kazo ka nemi aiki ko kwangila, zan nemi ka bani sakamakon zaben rumfarka, haka zan tambayi kowa saboda idan bamu yi haka ba, to ba zamu kai labari a zabe ba."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Hantar Atiku Ta Kaɗa, Wike Ya Yi Sabuwar Magana Kan Wanda Zai Goyi Baya a 2023

Atiku ya bayyana cewa ba zai yuwu dan kana zuwa wuraren kamfe ka nemi a baka Minista ko Kwangila ba, "Mu koma mazabu mu tabbatar mun yi nasara."

Daga cikin wadanda suka hallara a wurin sun hada da shugaban PDP na ƙasa, tsohon mataimakin shugaban kasa, gwamnonin PDP da jiga-jigai, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wane ɗan takara G5 zata goyi baya bayan raba hanya da Atiku?

A wani labarin kuma Gwamna Wike yace nan ba da jimawa ba kowa zai sna dan takarar shugaban kasa da G5 zata marawa baya

Gwamna Wike tare da wasu abokanansa gwamnonin PDP hudu dun haɗa tawagar G-5 kuma sun kauracewa duk wani taron kamfen Atiku Abubakar.

Sun kafa sharadin cewa dole a yi adalci a PDP ta hanyar sauya shugaban jam'iyya na kasa da wani ɗan kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel