2023: Kwamishinan Zabe Ya Bayyana Adadin Wadanda Zasu Kada Kuri’a a Kano

2023: Kwamishinan Zabe Ya Bayyana Adadin Wadanda Zasu Kada Kuri’a a Kano

  • Kwamishinan zabe na jihar Kano, Ambasada Zango Abd, ya sanar da cewa zai tabbatar da zaben gaskiya da adalci a fadin jihar Kano a 2023
  • Abdu yace shi ‘dan kowacce jam’iyyar siyasa ne kuma mutum 5,927,565 ne suka yi rijistar kada kuri’u a zaben dake gabatowa a jihar Kano
  • Yace suna biyayya ga sabbin dokokin zabe inda suka manna kwafin rijistar zabe a kowacce gunduma ta jihar domin ganin wadanda suka yi rijista

Kano - Sabon kwamishinan zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, Ambasada Zango Abdu, yace INEC ta shirya tsaf don aiwatar da zaben gaskiya a jihar a shekarar 2023.

Zaben Kano
2023: Kwamishinan Zabe Ya Bayyana Adadin Wadanda Zasu Kada Kuri’a a Kano. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Ya sanar da hakan ne yayin da kwamishinan zaben ya bayyana cewa a halin yanzu mutum 5,927,565 ne suka yi rijistar zabe a jihar Kano, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: An gayyaci Ganduje ya ba da shawari kan yadda za a yi zabe cikin lumana badi

Ambasada Abdu ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki wanda aka yi a dakin taro na Ofishin INEC na jihar a ranar Juma’a.

Yace INEC ta shirya tsaf wurin aiki da tanadin kundin tsarin mulki da sauran dokokin zabe da aka tanada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abdu yayi bayanin cewa, sashi na 19 sakin layi na 1 da na 2 na dokokin zaben 2022 sun bukaci hukumar da ta bayyana takardun rijistar masu zabe a kowacce karamar hukuma.

Ya jaddada cewa:

“Rijistar masu zabe a jihar Kano yanzu ta kai 5,927,565. Rijistar farko ce saboda sashi na 19 sakin layi na 1 da na 2 na dokokin zaben 2022 ya bukaci hukumar da ta bayyana kwafin rijistar masu zabe a kowacce gunduma da karamar hukuma.”

INEC ta fitar da kwafin rijistar zaben jama’a

Kwamishinan zaben ya bayyana cewa hukumar ta buga kwafin na takardu wanda yanzu haka an manna su a kowacce gunduma 484 da kananan hukumomi 44 na jihar.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Tsagin Gwamna Wike G5 Sun Gindaya Sharudda a Sabon Shirin Sulhu da Su Atiku

Abdu ya sanar da masu ruwa da tsaki cewa ya zo Kano ne domin aiwatar da zaben gaskiya da amana a zaben 2023 dake gabatowa.

Ya tabbatar da cewa shi ‘dan kowacce jam’iyyar siyasa ce kuma zai tabbatar da gaskiya da adalci ga dukkan wadanda zaben ya shafa.

“Hukumar zata tabbatar da cewa an yi wa kowacce jam’iyyar siyasa adalci a jihar kuma a basu damammaki iri daya. A don haka nake kira ga jam’iyyun siyasa da su zo wurin INEC a duk lokacin da suka ga dama su shigar da korafi, ofishin na aiki babu dare babu rana.”

- Yace.

Jaridar Independent ta rahoto cewa, sai dai yayi kira kan cewa hukumar zaben zata yi maganin duk wanda ta kama yana siyan katikan zabe kamar yadda dokar zabe ta tanada.

Sabon Kwamishinan ‘yan sanda yayi jawabi

A bangarensa, sabon kwamishinan ‘yan sandan da aka tura jihar Kano, Mamman Dauda, yace aikin hukumomin tsaro yana da kamanceceniya da na hukumar zabe.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Nanata, Ya Nuna a 2023, Mutanen Jiharsa Ba Za Su Duba Jam’iyya ba

“Aikinmu ya hada da tabbatar da an yi zabe babu tashin-tashina, na gaskiya da lumana.”

- CP Dauda yace.

Yace ‘yan sanda zasu tabbatar da cewa sun hada kai da hukumar INEC a zabe mai zuwa don a yi cikin kwanciyar hankali.

A bangarensu, wakilan jam’iyyun siyasa daban-daban sun bayyana farin cikinsu kan matsayar INEC wurin tabbatar da cewa an yi zaben 2023 tare da biyayya ga dokokin zabe.

IGP ya sabunta kwamishinonin ‘yan sanda a jihohi 8

A wani labari na daban, Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya canzawa wasu kwamishinonin ‘yan sanda wurin aiki a Najeriya.

Daga ciki kuwa har da jihar Kano inda ya aike CP Dauda Lawal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel