Gwamnan PDP Ya Nanata, Ya Nuna a 2023, Mutanen Jiharsa Ba Za Su Duba Jam’iyya ba

Gwamnan PDP Ya Nanata, Ya Nuna a 2023, Mutanen Jiharsa Ba Za Su Duba Jam’iyya ba

  • Gwamna Nyesom Wike yace kabila, addini, da jam’iyyar mutum ba za su cece shi a zaben 2023 ba
  • Mai girma Gwamnan ya nuna bai dace a ce ba za a zabi ‘dan takara ba saboda bangaren da ya fito
  • Wike ya nuna akwai bukatar kujeru da mukamai su rika zagayawa tsakanin ‘Yan Kudu da na Arewa

Rivers - Ba za ayi la’akari da kabilanci, jam’iyyar siyasa ko addini wajen zaben shugaban kasa a 2023 ba, wannan shi ne ra’yin Gwamna Nyesom Wike.

Da yake jawabi a lokacin da Adams Oshiomhole ya kaddamar da gada a Rumueprikon, The Nation ta rahoto Nyesom Wike yana batun zaben badi.

Tsohon shugaban APC ne ya kaddamar da gadar sama da Gwamnatin Wike ta gina a Obio-Akpor.

Gwamnan yace mutanen suna bukatar adalci, gaskiya da hadin-kai a daidai wannan marra, yace addini, kabilanci da jam’iyya ba za suyi tasiri a zaben 2023 ba.

Kara karanta wannan

Manyan Kudu maso Kudu Sun Fara Shirye-Shiryen Karya Bola Tinubu a Zaben 2023

Gwamna Nyesom Wike yake cewa ba daidai ba ne a ce ba za a zabi wasu ‘yan takara ba, saboda kurum lura da yanki, bangare, ko kuma addinin da suka rike.

Hadin-kai ake bukata - Wike

"Abin da muke nema a kasar nan shi ne hadin-kai, Najeriya ta zama daya. Ta haka ne kurum za mu rika yi wa junan mu kallon ‘yanuwan juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nyesom Wike
Nyesom Wike da Gwamnonin G5 Hoto: @GovWike
Asali: UGC

Muna bukatar Najeriyar da dukkanmu za mu iya alfahari da ita, zan san ba a dauke ni ‘dan bora ba, kowa yana da hakki daidai da ‘danuwansa.

- Nyesom Wike

Babu bukatar a rika cewa idan ba ka fito daga nan yankin ba, ba za mu zabe ka, ba mu son haka.

Wike yace sai an canza tunani

Wike bai kama sunan Atiku Abubakar ba, amma yace a 2023 babu ruwan mutane da jam’iyyar da mutum ya tsaya takara, muddin sun gamsu da shi.

Kara karanta wannan

Jagora a Jam’iyyar LP Ya Dawo APC, Yace Peter Obi Ba Za Su Kai Labari a 2023 ba

Gwamnan ya kuma nuna bai dace ayi watsi da ‘yan takaran wasu yankin kasar ba, babu mamaki yana magana ne a kan 'yan kudu da suke takara.

A rahoton, an ji Wike yana cewa dole a rika raba kujeru da adalci tsakanin Kudu da Arewa.

Tinubu ya yi tonon silili

An ji labari Asiwaju Bola Tinubu yace a cikin wadanda suke babatu saboda ya dauko Kashim Shettima, wasu sun nemi su zama abokan takararsa a 2023.

Sai dai har Tinubu ya gama jawabi, bai kama sunan wadanda suka sa ran zama ‘yan takaran mataimakin shugaban kasa a inuwar jam’iyya mai mulki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel