Rikicin PDP: Za A Cire Iyorchia Ayu? Atiku Ya Bayyana Matakinsa Na Karshe, Ya Aika Sako Ga Wike Da Saura

Rikicin PDP: Za A Cire Iyorchia Ayu? Atiku Ya Bayyana Matakinsa Na Karshe, Ya Aika Sako Ga Wike Da Saura

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya ce baya goyon bayan kiran da bangaren Wike ke yi na cire ciyaman din jam'iyyar, Iyorchia Ayu
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce cire shugaban jam'iyyar a yayin da ake fuskantar zabe ba hikima bane
  • Atiku, ya lura cewa duk da cewa ba a warware rikicin da ake yi a jam'iyyar, zai cigaba da yakin neman zabensa

Washington DC, Amurka - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce neman da ake yi ciyaman din jam'iyyar, Dr Iyorchia Ayu, ya yi murabus, ba lokacin da ya kamata bane kuma ba zai haifar da alheri ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a hirarsa da Muryar Amurka (VOA), Hausa a birnin Washington DC, ThisDay ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Nasarar APC Na Cikin Haɗari, In Ji Shugaban Kamfen Na Adamawa

Atiku in VOA
Rikcin PDP: Za A Cire Iyorchia Ayu? Atiku Ya Bayyana Matakinsa Na Karshe, Ya Aika Sako Ga Wike Da Saura. Hoto: @atiku.
Asali: Facebook

Abin da yasa ban goyi bayan cire Ayu ba, Atiku ya bayyana

Atiku ya ce bai goyi bayan cire Ayu ba a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa saboda, hakan ba dabara bane mai kyau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar shugaban kasar na PDP ya ce:

"Ba daidai ba ne a wannan lokacin mu yi tunanin sauya shugaban jam'iyyarmu, yayin da muke daf da shiga zabe."

Kamfen din 2023: Ba a warware rikicin PDP ba amma mun yi gaba, in ji Atiku

A wani abu da ya yi kama da sako ga gwamnonin PDP da ke ganin an zalunce su, karkashin jagorancin Nyesom Wike, Atiku ya ce ya fara kamfen dinsa na shugaban kasa duk da ba a warware rikicin jam'iyyar ba, Vangaurd ta rahoto.

An ambato yana cewa:

"Ba mu warware matsalar jam'iyyar ba. Amma mun yanke shawarar matsawa gaba. Jirgin mu ta tafi. Mun bar matsalolin a kwandon tarihi."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

A kokarin warware rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Mr Nyesom Wike na Jihar Rivers.

Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.

An yi ganawar ne a gidan gwamnatin Rivers da ke Asokoro a Abuja a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel