Mutuwar Ifeanyi: Kwankwaso, Hadimin Buhari Da Sanata Orji Kalu Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Davido Da Chioma

Mutuwar Ifeanyi: Kwankwaso, Hadimin Buhari Da Sanata Orji Kalu Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Davido Da Chioma

  • A ranar Litinin ne shahararren mawakin Najeriya, Davido Adeleke da budurwarsa, Chiom Rowlanda suka rasa dansu mai suna Ifeanyi
  • Yaron wanda ya shika shekaru uku a yan kwanaki da suka gabata ya nitse ne a cikin ruwa a gidan mawakin da ke Banana Island
  • Rabiu Kwankwaso, Orji Kalu da Bashir Ahmed sun aike da sakon ta’aziyyarsu ga mawakin da mahaifiyar yaron

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi’u Kwankwaso, ya mika ta’aziyyarsa ga shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido da budurwarsa, Chioma Rowland kan mutuwar dansu, Ifeanyi.

Ifeanyi dai ya nitse a cikin rafin wanka na shakatawa dake cikin gidansa dake unguwar Banana Island dake jihar Legas a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo

Kwankwaso, Ifeanyi da Bashir
Mutuwar Ifeanyi: Kwankwaso, Hadimin Buhari Da Sanata Orji Kalu Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Davido Da Chioma Hoto: Vanguard/Daily Post/PM News
Asali: UGC

Da yake martani a kan wannan mummunan al’amari da ya samu masoyan biyu a shafinsa na Twitter, Kwankwaso ya roki Allah da ya yiwa Davido da Chioma jagora a wannan mawuyacin lokaci.

Kwankwaso ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Zuciyata da addu’o’ina na tare da David Adeleke @davido da Chioma, a wannan mawuyacin lokaci.
“Allah yayi maku jagora sannan ya fitar da ku daga wannan lokaci nab akin ciki. – RMK.

Da yake martani kan lamarin, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya je shafinsa na Twitter don mika ta’aziyyarsa a kan mutuwar Ifeanyi.

Ya roki Allah a kan ya baiwa masoyan hakurin wannan babban rashi da suka yi.

Bashir ya rubuta:

“Tunanina da addu’o’ina na tare da @Davido, wanda ya rasa dansa, Ifeanyi. Kada Allah yasa kowasu iyaye su dandani radadin rashin da ta irin wannan mummunan al’amari.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Babbar Kungiyar Yarbawa da Gwamnan PDP

“Allah ya bashi hakuri da Chioma, mahaifiyar dan.”

Hakazalika, shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya mika ta’aziyyarsa ga iyakan Adeleke a kan wannan rashi da suka yi.

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter, Kalu ya ce yana cikin radadi da bakin cikin wannan rashi na Davido, yana mai cewa jama’a gaba daya zasu yi kewar dan mawakin.

Kalu ya kuma bayyana cewa ya soke duk wasu harkoki nasa na yau Talata, 1 ga watan Nuwamba domin alhinin rashin yaron cikin sirri. Ya kuma roki Allah ya amsa addu’o’in da aka yiwa Ifeanyi.

Ifeanyi: Yan Sanda Sun Kama Ma’aikatan Mawaki Davido Gaba Daya Kan Mutuwar Dansa

A gefe guda, mun ji cewa yan sanda sun kama dukkanin ma’aikatan gidan shahararren mawakin Najeriya, Davido kan mutuwar dansa, Ifeanyi.

Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da cewar dukkanin ma’aikatan na tsare a hannunsu don amsa tambayoyi, Sahara Reporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Dan Sanda Ya Sokawa Abokin Aikinsa Almakashi Yayin da Suke Baiwa Hammata Iska

Kakakin rundunar yan sandan jihar Lagas, Ben Hundeyin, ya fadama manema labarai a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba cewa ana nan ana gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a mutuwar yaron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel