Tinubu Ya Bayyana Sunan Da Babban Malamin Addinin Kirista Ya Nada Masa, Tare Da Ma'anar Sunan

Tinubu Ya Bayyana Sunan Da Babban Malamin Addinin Kirista Ya Nada Masa, Tare Da Ma'anar Sunan

  • Jagoran jam'iyyar jam'iyyar All Progressives Congress, APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce Fasto Enoch Adeboye ya nada masa suna Ibrahim (Abraham)
  • Tinubu, wanda kuma shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya ce shugaban na RCCG ya nada masa sunan ne lokacin da aka rantsar da matarsa, Remi Tinubu, matsayin fasto
  • Tsohon gwamnan na jihar Legas, a ranar Litinin 24 ga watan Oktoba, a Kano ya ce ya tambayi Adeboye mene sunan ke nufi, malamin addinin ya ce masa mahaifin dukkan kasashe

Kano - Asiwaju Ahmed Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba ya ce Fasto Enoch Adeboye na Redeemed Christian Church of God, RCCG, ya nada masa sunan kirista, Abraham.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Jiga-Jigan 'Yan PDP Da Suka Yi Watsi Da Atiku Suka Rungumi Obi

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da kungiyar kiristoci na Najeriya, CAN, reshen jihar Kano.

Bola Tinubu
Tinubu Ya Bayyana Sunan Da Babban Malamin Addinin Kirista Ya Nada Masa, Tare Da Ma'anar Sunan. (Photo: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce a yayin da ya tambayi Fasto Adeboye ma'anar sunan, malamin ya fada masa ma'anar sunan shine mahaifin dukkan kasashe.

Dan takarar shugaban kasar na APC ya ce abin ya faru a ranar da aka nada matarsa, Sanata Remi Tinubu, matsayin fasto a cocin na RCCG.

Kalamansa:

"A ranar da aka nada matata a matsayin fasto, ina wurin. Fasto Adeboye ya nada min suna Abraham. Na tambaye shi ma'anar? Ya ce, mahaifin dukkan kasashe."

Kalli bidiyon a kasa:

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

Duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Musulmi da Kirista duk daya ne: Tinubu ya yiwa malaman addini jawabi a Kano

Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.

A yayin da ta ce a arewa ne za a ci zabe ko a sha kaye, Musawa ta ce akwai yiwuwar tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya ci jihohi kamar Benue, Plateau da Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel