Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE Kacal
Gabanin babban zaben shekarar 2023, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar da jerin sunaye na karshe ne yan takarar shugaban kasa.
A cewar jerin sunayen, jam'iyyun siyasa 18 ne za su fafata a babban zaben da ake shirin yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.
Daga cikin yan takarar 18, guda biyu sun yi rajista da shaidar kammala makarantar frimare (FLSC) da ta kammala sakandare wato WAEC/SSCE, yayin da sauran suka yi rajista da HND, B.Sc da wasu manyan digiri, ciki har da MSc da PhD.
Legit.ng ta lura cewa yin rajista da kananan digiri ba ya nufin wani ya fi wani idan har dai digirin na cikin wadanda kundin tsarin mulki ta amince da su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya
Kafin a zabi mutum matsayin shugaban kasa a Najeriya, kundin tsarin mulki na 1999, sashi na 131, ya ce dole dan takarar ya yi karatu zuwa a kalla matakin kammala frimare.
2023: Wane sharruda ake bukatan cika wa kafin a iya zaben mutum matsayin shugban Najeriya?
Ga abubuwan da doka ta buka mutum ya cika kafin zama shugaban kasar Najeriya bisa, kundin tsarin mulki
- Ya kasance haifafan dan Najeriya ne
- Ya kasance ya kai shekaru a kalla 35;
- Ya zama mamba na jam'iyyar siyasa kuma jam'iyyar na daukan nauyinsa; kuma
- Ya yi karatu zuwa a kalla matakin satifiket ko abin da ya yi dai-dai da shi.
1. Kachikwu Dumebi
Kachikwu Dumebi shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress, (ADC).
Dan shekara 48 ya mika takardar FLSC da WAEC a matsayin takardun karatunsa.
2. Nnadi Charles Osita
Nnadi Charles Osita shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Peoples Party, (APP).
3. Ojei Princess Chichi
Ojei Princess Chichi ita ce yar takarar shugaban kasa na jam'iyyar Allied Peoples Movement, (APM).
Chichi ce yar takarar shugaban kasa mace tilo a zaben. Ta mika takardar kammala sakandare a daga makarantar American International a Switzerland.
A lura cewa wasu yan takarar suna da manyan takardun karatu amma saboda dalilan da su kadai suka sani, suka zabi su mika FSLC, NECO da WAEC tunda doka ta amince da hakan.
Yan takarar mataimakan shugaban kasa da suka mika SSCE kawai
1. Kyabo Yahaya Muhammad
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar National Rescue Movement, NRM.
FSLC da SSCE ya mika a cewar jerin sunayen da INEC ta fitar.
2. Johnson Emmanuel Chukwuka
Shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Action Alliance, AA. WAEC ya mika wa INEC.
3. Zego Haro Haruna
Zego shine mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PRP.
FSLC da WAEC ya mika wa INEC.
4. Buhari Muhammad Ahmed
Buhari Muhammad Ahmed shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC.
FSLC da WAEC ya mika wa INEC.
Asali: Legit.ng