Matsalolin Najeriya Sun Fi Karfin Tsoho Dan Shekara 70, Inji Matashin Dan Takara

Matsalolin Najeriya Sun Fi Karfin Tsoho Dan Shekara 70, Inji Matashin Dan Takara

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Accord ya caccaki masu neman gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Farfesa Chris Imulomen ya ce, kasar nan bata dace da shugaban da ya kai shekaru 70 ba, matashi ya kamata a zaba
  • Chris dai shi ne dan takarar shugaban kasa mafi karancin shekaru daga cikin wadanda za su gwabza a zaben 2023 mai zuwa

Kano - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Accord Farfesa Chris Imulomen ya bayyana cewa, kalubalen da Najeriya ke fuskanta sun fi karfin shugaba mai shekarun da suka 70 wajen warware su, rahoton jaridar The Guardian.

A cewar farfesan, Najeriya na bukatar matashi mai jini a jika dake kan ganiyar kuruciya domin ba da jininsa wajen nemo mafita ga kasar.

Dan takarar shugaban kasa ya ce tsoffi ba za su iya kawo mafita ga Najeriya ba
Matsalolin Najeriya sun fi karfin tsoho dan shekara 70, inji matashin dan takara | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da jam'iyyarsu ta gudanar a jihar Kano, inda yace babbar matsalar Najeriya rarrabuwar kai ne.

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Matsalolin Najeriya na bukatar matashi mai jini a jika ya magance su. Ni kadai ne dan takarar da zai iya magance rashin tsaro; da zai dakile zaman banza; da zai tafi tare da dukkan 'yan Najeriya. Babu bambanci tsakanin matasa daga Arewacin Najeriya da Kudacinta."

A cewarsa, jam'iyyar Accord ce kadai jam'iyyar dake nuna alamar hadin kai; don haka shugaban kasa daga jam'iyyar zai tabbatar da hadin kan 'yan kasa baki daya.

Vanguard ta naqalto shi yana cewa:

"Idan kuna da shugaban kasan da ya fito daga jam'iyyar Accord, shin kun san ma'anar Accord? Accord na nufin kadaitaka da ci gaba. Jam'iyyar na nufin hadin kai."

Najeriya Ta Zabi Canji a 2015, Amma Ta Kare da Talauci da Rashin Tsaro

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, zai kawo karshen talauci da rashin tsaro a Najeriya idan aka zabe shi a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 10 ga watan Oktoba yayin kaddamar da kamfen dinsa a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, rahoton TheCable.

Atiku, wanda ya saki APC a 2017 ya ce a lokacin da PDP ke mulki, ta dago Najeriya daga zuwa sama kuma ta kai kasar matsayin mafi kyawun tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel